Da duminsa: Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Sojoji 24 a kasar Chadi
- Yan ta'addan Boko Haram sun kai mumunan hari Chadi
- A Najeriya kuwa sama da yan kungiyar 100 sun mika wuya
- Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan Sojin Najeriya da Chadi
Akalla Sojojin kasar Chadi 24 sun rasa rayukansu a daren 4 da 5 na watan Agusta a wani hari da yan ta'addan boko Haram suka kai a yankin tafkin chadi, kamar yadda kafafen yada labaran a Chadi suka ruwaito ranar Alhamis.
Mai magana da yawun rundunar sojin, Azem Bermandoa Agouna, ya tabbatar da hakan a Tchoukoutalia, Lac, yayinda jaridar Xinhua ta tuntubesa.
Kaakin Sojin ya ce sun ce suna kan hanyar daukar fansa.
Yankin Lac ya kasance babban inda yan Boko Haram ke kai hari.
A watan Afrilu, yan ta'addan sun kai hari Chadi inda suka hallaka Soji kimanin 90.
Karin yan Boko Haram 19 sun mika wuya ga jami'an Sojoji a Borno
A bangare guda, an samu sabon nasara a yaki da yan ta'adda yayinda wasu yan Boko Haram/ISWAP suka mika wuya ga rundunar FOB dake Bama, jihar Borno.
A jawabin da Diraktan yada labarai na hukumar Soji, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya saki ranar Laraba, 4 ga Agusta, yace mayaka 14 tare da iyalansu suka mika wuya.
Nwachukwu ya ce Sojojin sun karbi tubabbun yan ta'addan ne a cikin dajin Sambisa ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng