Karin yan Boko Haram 19 sun mika wuya ga jami'an Sojoji a Borno
1 - tsawon mintuna
- Jami'an Sojojin Najeriya sun samu gagarumin nasara a Arewacin Najeriya
- Hukumar ta sanar da mika wuyan wasu yan ta'addan Boko Haram da iyalinsu
- Kakakin hukumar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba
An samu sabon nasara a yaki da yan ta'adda yayinda wasu yan Boko Haram/ISWAP suka mika wuya ga rundunar FOB dake Bama, jihar Borno.
A jawabin da Diraktan yada labarai na hukumar Soji, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya saki ranar Laraba, 4 ga Agusta, yace mayaka 14 tare da iyalansu suka mika wuya.
Nwachukwu ya ce Sojojin sun karbi tubabbun yan ta'addan ne a cikin dajin Sambisa ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta.
Yace:
"Yan ta'addan sun hada da maza mayaka 19, mata 19 da yara 49 yan garin Njimia kuma sun ajiye makamansu."
"Yan ta'addan da iyalansu yanzu haka na hannun jami'ai don gudanar da bincike kansu, yayinda aka yiwa yaran rigakafin shan inna."
Shugaban Sojin kasa, Faruk Yahaya, ya jinjinawa Sojoji bisa wannan nasara da suka samu.
Asali: Legit.ng