Bayan shekaru 7, ban fidda rai za'a ceto 'yan matan Chibok ba: Gwamna Babagana Zulum

Bayan shekaru 7, ban fidda rai za'a ceto 'yan matan Chibok ba: Gwamna Babagana Zulum

- Yau shekara bakwai kenan dai-dai tun sanda mayaƙan Boko Haram ɗin suka kai farmaki GGSS Chibok

- An sace daliban makarantar Chibok ne ranar 14 ga watan Afrilu, 2014

- Tun daga lokacin, an samu ceto kimanin 82 cikin daliban

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya ce da sannu za'a ceto dalibai matan da yan ta'addan Boko Haram suka sace a makarantar sakandaren Chibok a 2014.

Zulum ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki bayan shekaru bakwai da yan Boko Haram sukayi awon gaba da daliban yayinda suke shirin rubuta jarabawa.

Duk da cewa an ceto wasu daga cikin yaran, har yanzu akwai sauran daliban na hannun yan ta'addan.

A cewar Zulum, a matsayinsa na uba, ba zai iya jure ciwon rasa diya mace tsawon shekaru bakwai hannun yan ta'adda ba.

Ya yi kira ga ayi addu'a ga yan matan Chibok da sauran mutanen dake tsare hannun yan ta'adda su samu yanci.

KU DUBA: A karon farko, Gwamnan Nasarawa ya rantsar da mace a matsayin babbar Alkalin jihar

Bayan shekaru 7, ban fidda za'a ceto 'yan matan Chibok: Gwamna Babagana Zulum
Bayan shekaru 7, ban fidda za'a ceto 'yan matan Chibok: Gwamna Babagana Zulum Credit: @GovBorno
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa 6 Zasu haɗa ƙarfi-da-ƙarfe Wajen yaƙar yan Ta'adda a Yankunan su

A cewar gwamnan, "A matsayin na uban yan mata, ban tunanin zan iya jure zafin kasancewar diyata hannun yan ta'adda na tsawon shekaru bakwai."

"Gaskiya, gwamma mutum ya rasa diyarsa da ace tana hannun yan Boko Haram."

"A matsayina na uban kowa a Borno, ban fidda ran za'a ceto sauran yan matan Chibok da sauran wadanda ke rike hannun Boko Haram ba."

A bangare guda, iyayen ragowar ɗalibai mata 112 da aka sace a makarantar sakandiren mata dake Chibok jihar Borno, sun bayyana cewa suna son ganin yayan su kafin su mutu.

Tunda mayaƙan Boko Haram dake biyayya ga Abubakar Sheƙau suka sace yayan nasu, wasu daga cikin iyayen sun rasu saboda tashin hankali wasu kuma sun rasu saboda lokaci yayi.

Yau shekara bakwai kenan dai-dai tun sanda mayaƙan Boko Haram ɗin suka kai farmaki GGSS Chibok ranar 14 ga watan Afrilu, 2014.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel