Ngige: Na ja kunnen 'ya'yana likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali

Ngige: Na ja kunnen 'ya'yana likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali

  • Ministan kwadago Chris Ngige, ya ce ya ja kunnen 'ya'yansa likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali
  • Ngige ya bayyana cewa ba zai cigaba da sasanci da likitoci ba, zai dauka matakin hana su albashi idan har basu koma aiki ba
  • Ministan yace ya gana dasu har sau biyu, don haka yana da wasu ayyuka a gabansa, ba zai cigaba da bata lokacinsa ba

FCT, Abuja - Chris Ngige, ministan kwadago na Najeriya yace ya ja kunnen 'ya'yansa likitoci da kada su kuskura su shiga wannan yajin aikin da ake yi wanda ya kwatanta da "rashin hankali".

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta shiga yajin aiki saboda zargin gwamnatin tarayya da take da karya yarjejeniyar da suka yi da kungiyar, Daily Trust ta ruwaito.

Ngige: Na ja kunnen 'ya'yana likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali
Ngige: Na ja kunnen 'ya'yana likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali. Hoto daga sunnewsonline.com
Asali: UGC

Kokarin da gwamnatin take yi na ganin cewa likitocin sun janye yajin aikin da suka fada ya gagara.

Kara karanta wannan

IBB: Dole ne shugaban kasa na gaba ya kasance masanin tattalin arziki

Wanne mataki gwamnatin tarayya za ta dauka?

Amma yayin magana da Channels TV shirin siyasarmu a yau na daren Juma'a, Ngige ya ce yana da 'ya da 'da da suke likitoci ne a kasar nan.

Ministan ya sha alwashin amfani da karfin iko kan likitcoin idan suka cigaba da wannan yajin aikin. Ya ce in har suka ki komawa bakin aiki nan da mako na gaba, zai saka dokar babu biya.

A mako mai zuwa zan tada wannan al'amarin saboda sasanci ya ki aiki.
Ba zan sake ganawa dasu ba saboda ina da abubuwan yi. Sasanci biyu nayi jiya, zan cigaba da bata lokacina a kansu ne?
Ina da wasu mafita a cikin dokokin kwadago kuma zan yi amfani dasu. Zan yi amfani da sashi na 43. Na sanar da NARD ba zasu samu albashi ba a yayin da suke yajin aiki kuma ba zai taba shiga cikin tarinsu na fansho ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

Ko a dokokin kwadago na duniya, an goyi bayan hakan saboda suna tsayar mana da ayyukan da suka zama dole. Bai dace su shiga yajin aiki ba ba tare da sun sanar damu ba ana sauran kwanaki 15.
Abubuwa zasu sauya nan da mako mai zuwa. Su jira su gani, gwamnati suke so gwadawa. Suna wasa da rayuka. Na ja kunnen 'ya'yana likitoci da kada su shiga yajin aikin rashin hankalin nan.

Ya gwamnatin tarayya zata yi idan babu likitoci?

A yayin da aka tambaye shi ko gwamnatin tarayya zata iya al'amura babu likitoci balle a yanzu da aka samu barkewar korona da amai da gudawa, Ngige yace sun shawo kan komai.

Ya kara da dora laifi kan gwamnatocin jiha inda yace jama'a suna magana kan gwamnatin tarayya ne kadai ba tare da sun duba na jihohi ba.

Rashawa tayi katutu a gwamnatinka fiye da lokacin mulkina, IBB ga Buhari

Kara karanta wannan

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce yayi yaki da rashawa fiye da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasan Najeriya ya sanar da hakan ne yayin da tattauna da Arise TV a ranar Juma'a.

Ya ce mutanen da suka yi aiki a kasan shi waliyyai ne idan aka dangantasu da wadanda a halin yanzu suke mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel