Da duminsa: Rashawa tayi katutu a gwamnatinka fiye da lokacin mulkina, IBB ga Buhari

Da duminsa: Rashawa tayi katutu a gwamnatinka fiye da lokacin mulkina, IBB ga Buhari

  • Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida, yace ya yaki rashawa fiye da shugaba Buhari
  • Ya kara da cewa wadanda suka yi mulki karkashinsa waliyyai ne idan aka alakantasu da mulkin Buhari
  • Tsohon shugaban kasan ya ce an bibiyi wanda ya saci N313,000 amma wadanda suka saci biliyoyi suna yawo a gari

Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce yayi yaki da rashawa fiye da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasan Najeriya ya sanar da hakan ne yayin da tattauna da Arise TV a ranar Juma'a.

Da duminsa: Rashawa tayi katutu a gwamnatinka fiye da lokacin mulkina, IBB ga Buhari
Da duminsa: Rashawa tayi katutu a gwamnatinka fiye da lokacin mulkina, IBB ga Buhari
Asali: Original

Ya ce mutanen da suka yi aiki a kasan shi waliyyai ne idan aka dangantasu da wadanda a halin yanzu suke mulki.

Tsohon shugaban mulkin sojan ya sanar da yadda aka yaki tsohon gwamnan mulkin soja wanda yayi waddaka da N313,000, amma aka bar wadanda suka saci biliyoyin naira suna yawo a garo.

Kara karanta wannan

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

A yayin da aka tambaye shi ko ya yadda da wadanda suka ce gwamnatinsa ta wawuri kudi, ya ce:

Amma abinda ke faruwa a yanzu yafi muni kan abinda ya faru yayin da nake mulki... Mu waliyyai ne idan aka danganta mu.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel