Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

  • Karamin ministan ilimi ya bayyana dalilin da yasa gwamnati ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba
  • A cewar gwamnati, hakan na kara karfafa 'yan bindiga, kuma suna kara sayen makamai don addabar jama'a
  • Ya bayyana cewa, gwamnati na daukar matakan da suka dace domin ganin an samu mafita game da matsalar tsaro

Karamin Ministan Ilimi, Cif Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana dalilan da suka sa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da batun tattaunawa da masu garkuwa da dalibai a Najeriya.

Nwajiuba ya yi magana ne ranar Laraba 4 ga watan Agusta yayin amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar gwamnati bayan zaman Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa, Abuja.

Ya ce 'yan bindiga suna amfani da kudaden da suka tara daga biyan kudin fansa wajen tayar da kayar baya, wanda hakan ya haifar da rashin tsaro a kasar.

Karamin ministan ilimi ya magantu kan biyan kudin fansa
Cif Chukwuemeka Nwajiuba | Hoto: edufirst.ng
Asali: UGC

Da yake magana kan abin da gwamnati ke yi kan bidiyon da ya bazu inda wasu masu garkuwa da mutane ke azabtar da wasu daga cikin daliban da aka sace a jihar Kaduna, Nwajiuba ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ana kokarin ceto yaran.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Legit Hausa ta tattaro daga Daily Trust, inda ministan ke cewa:

“Gaskiyar magana, abin takaici ne a duk lokacin da aka sace wani dalibin mu a kowane lokaci, ina tabbatar muku da cewa gwamnatin tarayya na yin duk mai yiyuwa. Mun yi tarurruka da dama tare da jami'an tsaron mu da kuma na wannan yankin baki daya.

Da aka tambaye shi ko akwai matakan da za a bi don ganin makarantun gwamnatin tarayya sun kubuta daga harin ‘yan bindiga, Ministan ya ce:

“Na riga na fada cewa duk hanyoyin ne gwamnati ke bi wajen gudanar da aikin tsaro ba wai kawai a makarantun mu ba.
“Na’am, gwamnatin tarayya ta mallaki wasu kwalejojin tarayya a kewayen Najeriya, daga cikin makarantun sakandare 25,000; Gwamnatin tarayya ta mallaki 120 ne kacal.

Ya ce gwamnati na daukar matakan tabbatar da tsaro a makarantun.

“Amma ba mu takaita kanmu ga cibiyoyin mu ba kadai; muna duba tsaro kamar yadda manufar kasa gaba daya aikin gwamnati ne.”

Kara karanta wannan

Kai tsaye ta gidan talabijin, ministan Buhari yana rokon 'yan bindiga alfarma

Gwamna ya rushe gidan da masu garkuwa suka ajiye matar kwamishina da direbanta a Benue

Makurdi, Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue ya bada umurnin a rushe gidan da yan sanda suka kashe mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sannan suka ceto matar kwamishina da direbanta.

Legit.ng a baya ya ruwaito cewa jami'an tsaron Operation Zenda a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta sun kashe masu garkuwa da mutane biyu suka ceto Mrs Ann Unnege, matar kwamishinan kasa da sifiyo.

The Punch ta ruwaito cewa Gwamna Samuel Ortom wanda daga bisani a ziyarci hedkwatar yan sanda a Makurdi ya bada umurnin a rushe gidan da aka ajiye wadanda aka yi garkuwan da su.

Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta cafke wani barawon shanu mai shekaru 16, Umaru Muhammed, kan garkuwa da mutane a Ibadan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sunfi IPOB da Igboho hatsari - Tsohon Sanata

Muhammad ya amsa cewa yana cikin gungun masu garkuwa da mutane yayin da yake amsa tambayoyi a hedkwatar rundunar, Eleyele, Ibadan, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa,wanda suka yi awon gaba dashi na karshe sun rude shi da ya zo ya sayi shanu ne a kauyen Akinyele, Karamar Hukumar Akinyele a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Wanda ake zargin da ya amsa cewa shi barawon shanu ne ya ce wasu abokan aikinsa da a yanzu suke nemansa sun ce ya kira mutane su zo su sayi shanu a wurinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.