IBB: Dole ne shugaban kasa na gaba ya kasance masanin tattalin arziki

IBB: Dole ne shugaban kasa na gaba ya kasance masanin tattalin arziki

  • Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya ce kamata yayi Najeriya ta samu masanin tattalin arziki a matsayin shugaban kasa
  • Kamar yadda ya bayyana a yayin da ake tattaunawa da shi, wanda ya fahimci Najeriya da 'yan Najeriya ne ya dace da jagorancin kasar
  • IBB ya shawarci gwamnati mai ci a yanzu da su bude hanyoyin inganta tattalin arziki tare da amfani da baiwar da Ubangiji ya baiwa kasar

Tsohon shugaban kasan mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida wanda ake kira da IBB, ya ce ya kamata shugaban kasan Najeriya na gaba ya kasance mai fahimta a fannin tattalin arziki.

A yayin tattaunawa da Arise TV a ranar Juma'a, ya ce ya ga wasu mutanen dake da wannan nagartan kuma ya dace a ce sune suka samu shugabanci.

IBB: Dole ne shugaban kasa na gaba ya kasance masanin tattalin arziki
IBB: Dole ne shugaban kasa na gaba ya kasance masanin tattalin arziki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Waye ya dace da shugabancin kasar nan?

Idan muka samu shugaban mai nagarta dake alaka da mutane kuma yana kokari wurin magana da jama'a ba wai mai magana kan jama'a ba, tabbas komai zai daidaita.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

Na fara hango shugaba mai nagarta ga 'yan Najeriya. Wannan shine mutumin dake yawo a kasar nan kuma yana da aboki a duk inda yaje kuma ya san a kalla mutum daya da zai yi magana da shi.
'Yan Najeriya suna da jajircewa, don haka dole ne shugabanni su yi amfani da hakan wurin cimma manufofinsu.
Wannan shine mutumin da yake da ilimi a fannin tattalin arziki kuma dan siyasa nagari, wanda zai iya yi wa 'yan Najeriya magana da sauransu. Shugabannin ya dace su fahimci Najeriya da 'yan Najeriya. Duk wanda yake son zama shugaba dole ne yayi amfani da hazakarsa domin fahimtar jama'a.

Za a samu mai irin nagartar da IBB ya bayyana?

A yayin da aka tambaya ko yana tunanin za a iya samun irin wannan a 2023, ya ce ya yadda za a samu irin shi.

IBB ya shawarci gwamnatin nan da ta gyara salonta a fannin tattalin arziki, inda yace:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

An kanainaye hanyoyin da tattalin arzikin kasar nan ke tafiya. Mu bude duk hanyoyin inganta tattalin azriki kuma mu yi amfani da baiwar da Ubangiji yayi mana.

Ya dora laifin tabarbarewar tsaron kasar nan da shugabannnin yanzu.

Rashawa tayi katutu a gwamnatinka fiye da lokacin mulkina, IBB ga Buhari

Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce yayi yaki da rashawa fiye da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasan Najeriya ya sanar da hakan ne yayin da tattauna da Arise TV a ranar Juma'a.

Ya ce mutanen da suka yi aiki a kasan shi waliyyai ne idan aka dangantasu da wadanda a halin yanzu suke mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel