IBB ya bayyana mummunan lamarin da zai auku da ba a soke zaben 12 ga watan Yuni ba

IBB ya bayyana mummunan lamarin da zai auku da ba a soke zaben 12 ga watan Yuni ba

  • Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban kasa na mulki soja, ya bayyana dalilinsa na soke zaben 12 ga watan Yuni
  • Ibrahim Babangida ya tabbatar da cewa babu shakka mummunan juyin mulki za a tafka da ba a soke zaben ba
  • A cewarsa, dole ce tasa yayi amfani da wannan salon na 'Maradona' domin tseratar da kasar nan daga rikici

Tsohon shugaban kasan mulki soja, Ibrahim Babangida ya kara yin magana kan soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 inda yace babu shakka mummunan juyin mulki za a tafka a kasar nan da ba a soke shi ba.

Zaben an yi shi ne tsakanin Bashir Tofa na jam'iyyar National Republican Convention (NRC) da MKO Abiola na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

IBB ya bayyana mummunan lamarin da zai auku da ba a soke zaben 12 ga watan Yuni ba
IBB ya bayyana mummunan lamarin da zai auku da ba a soke zaben 12 ga watan Yuni ba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Me ya faru a ranar 12 ga watan Yunin 1993?

Duk da Abiola ne ya ci zaben kamar yadda sakamako ya nuna, an soke zaben tun kafin jami'ai su bada sanarwan wanda yayi nasara.

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

Wannan al'amari kuwa ya janyo abubuwa da yawa saboda wasu jama'a sun fita titi zanga-zanga.

Amma a yayin tattaunawa da ARISE TV a ranar Juma'a, IBB ya ce ba a yi mummunan juyin mulki bane sakamakon "Yadda muka bi salon Maradona muka shawo kan lamarin."

Kamar yadda tarihi ya nuna, zaben 12 ga watan Yuni ne zabe mafi gaskiya da inganci da aka taba yi a Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama wanda yayi nasarar zaben inda ya mayar da ranar 12 ga watan Yuni ta zamo ranar damokaradiyya a kasar nan.

Me zai faru da ba a soke zaben ba?

A yayin da aka bukaci yayi tsokacin kan zaben, IBB ya ce:

Kuna son in fada muku gaskiya? Da ace ba a soke wannan zaben ba, babu shakka mummunan juyin mulki za a yi wanda zai janyo tarzoma, abinda zan iya tabbatar muku kenan.

Kara karanta wannan

Ana batun karbar cin hancin Abba Kyari, magajin shi zai karbi kyautar $10,000

Babu shakka hakan zai sake rikita kasar nan," yace yayin da yake tabbatar da cewa matsalar daga sojoji ce da kuma wajensu.

Rashawa tayi katutu a gwamnatinka fiye da lokacin mulkina, IBB ga Buhari

Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce yayi yaki da rashawa fiye da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasan Najeriya ya sanar da hakan ne yayin da tattauna da Arise TV a ranar Juma'a.

Ya ce mutanen da suka yi aiki a kasan shi waliyyai ne idan aka dangantasu da wadanda a halin yanzu suke mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel