Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane

Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Oyo sun cafke wani matashi dake aikin satar shanu da garkuwa da mutane
  • Matashin ya bayyana yadda ya shiga harkar tare da bayyana wadanda suka nuna masa mummunar sana'ar
  • A halin yanzu an kama shi tare da wani abokin harkallarsa yayin da aka kuma gabatar dasu ga manema labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta cafke wani barawon shanu mai shekaru 16, Umaru Muhammed, kan garkuwa da mutane a Ibadan.

Muhammad ya amsa cewa yana cikin gungun masu garkuwa da mutane yayin da yake amsa tambayoyi a hedkwatar rundunar, Eleyele, Ibadan, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa,wanda suka yi awon gaba dashi na karshe sun rude shi da ya zo ya sayi shanu ne a kauyen Akinyele, Karamar Hukumar Akinyele a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Wanda ake zargin da ya amsa cewa shi barawon shanu ne ya ce wasu abokan aikinsa da a yanzu suke nemansa sun ce ya kira mutane su zo su sayi shanu a wurinsa.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a jihar Kano

Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane
'Yan sandan Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Dangane da yadda ya sami damar gudanar da aikin, wanda ake zargin ya ce:

“An nemi in kira kwastomomi na su zo su sayi shanu. Sannan, na kira Taofeek kuma ya zo ya same ni a kauyen mu. Amma a kan hanyarmu ta zuwa wani kauye, mutanena suka kawo mana hari.
“Mun tsara mu sace su don neman kudin fansa amma abin takaici wasu matasan kauye suka dakile shirin. An kawo karshen shirin harbe-harbe kuma an kashe daya daga cikin matasan kauyen a cikin farmakin."

Ban taba garkuwa da mutane ba

A cewarsa, bai taba garkuwa da mutane ba a baya amma mutanensa kan yi hakan sau da yawa, wanda da yawa daga cikinsu ya ce sun gudu.

Ya kara da cewa:

“Sun gayyace ni in shiga aiki tare da su kuma sun ba ni dabarar da zan yi amfani da ita. Sun yi min barazanar cewa idan ban ba su hadin kai ba, za su yi magani na kuma sun tilasta ni in yi abinda suka umarce ni.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rushe gidan da masu garkuwa suka ajiye matar kwamishina da direbanta a Benue

"Daya daga cikin mutanena da muka shirya aikin tare an kama shi nan take kuma kama shi ne ya kai ga kama ni."

Da yake gabatar da wadanda ake zargin gaban manema labarai, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ngozi Onadeko, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Usman Mohammed mai shekaru 27, da Umaru Mohammed mai shekaru 16.

Ngozi ta ce a ranar 9 ga Yuli, 2021, wani Taofeek Olaide ya sami kiran waya daga wani mutum Umaru Mohammed, yana mai cewa yana da shanu don sayarwa bisa umarnin mahaifinsa a kasuwar Kara, yankin Akinyele a Ibadan.

Sarki a arewacin Najeriya ya ba Fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 su bar jiharsa

Sarkin masarautar Muri a jihar Taraba, Abbas Tafida ya ba da wa’adin kwanaki 30 ga makiyaya da ke addabar mazauna jihar kan su bar dazuzzukan fadin jihar ko kuma a tilasta musu yin hakan.

Kara karanta wannan

An Kama Wanda Ake Zargi Da Ɗaukan Nauyin Ƴan IPOB/ESN, Da Wasu Mutum 25 a Otel

Gidan talabijin na Channels ta ce, Sarkin ya bayar da wa'adin ne a ranar Talata bayan sallar Idi.

Wannan ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, da hare-hare a jihar da wasu miyagu da ake zargin makiyaya ne ke aikatawa.

Ya yi ikirarin cewa Fulani makiyaya ne ke da alhakin aikata laifuka a jihar don haka ya kamata su bar dazuzzukan da ke cikin jihar cikin kwanaki 30 ko kuma a tilasta musu fita.

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

A wani labarin, Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama kunshin tabar wiwi 404 da darajarsu ta kai miliyan 32 a jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kuma kwace wasu haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai Naira miliyan 234 daga shiyyar a zango na biyu na shekarar 2021.

Da yake nuna abubuwan a Sakkwato da Kebbi bi da bi a ranar Laraba, Mataimakin Kwanturola Olurukoba Oseni Aliyu, ya ce sauran kayayyakin da aka kwace sun hada da, shinkafa, jarakunan man fetur, katan din taliya da daurina yadi.

Kara karanta wannan

Yanzu: Rikici ya barke tsakanin dan Shi'a da mazauna a Kano, ya jawo kone-kone

Asali: Legit.ng

Online view pixel