Yadda Allah Ya yi barazanar shafe ni daga doron kasa, shahararren malamin addini ya bayyana

Yadda Allah Ya yi barazanar shafe ni daga doron kasa, shahararren malamin addini ya bayyana

  • Shahararren faston nan na Najeriya, Fasto Enoch Adeboye, ya yi ikirarin cewa Allah ya taba koya masa darasi game da shawo kan girman kai
  • Babban jagoran na Cocin Redeemed Christian Church of God ya ce haduwar da ya yi da Allah ya shiryar da shi ta dukkan hanyoyinsa
  • Faston ya bayyana cewa wasu mutane sun tambaye shi yadda ya yi ya kasance mai tawali'u duba da duk abin da Allah ya yi masa

Babban jagoran cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya yi ikirarin cewa ya taba samun gargadi mai tsanani daga Allah game da girman kai.

A cewar PM News, mai wa'azin ya yi iƙirarin cewa Allah ya taɓa yin barazanar kawar da shi daga doron ƙasa idan har yayi alfahari.

Yadda Allah Ya yi barazanar shafe ni daga doron kasa, shahararren malamin addini ya bayyana
Fasto Adeboye ya ce Allah Ya yi barazanar shafe shi daga doron kasa idan ya kasance mai girman kai Hoto: Pastor EA Adeboye
Asali: Facebook

An tattaro cewa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Agusta, a babban taron shekara-shekara na coci karo na 69.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 1 da tunbuke shi, Sanusi II ya fadi abin da ya sa ya zabi ya bar gadon mulki

Shugaban Kiristocin ya ce haduwar da yayi da Allah ta sa ya ci gaba da kasancewa da tawali'u ba tare da la’akari da nasarorin da ya samu ba.

Da yake magana kan gamuwar, ya ce:

“Zan tunatar da ku abin da ya faru bayan Lekki 98 ′ ɗaya daga cikin manya manyan taron a muka taɓa gudanarwa. Mun dawo nan da daddare, na fita ina yabon Allah saboda manyan abubuwan da ya yi tsakanin 2:00 na safe zuwa 3:00 na safe, na san wurin da nake, Ya ce ya dana, ka durƙusa, cikin sauri na sunkuya sannan Ya ce zana siffar mutum a cikin rairayi, da sauri na yi.
"Kuma Ya ce tashi, na yi, Ya ce goge abin da ka zana da kafa, na yi, Ya ce dana, idan ka manta ko wane ne mai kula, zan shafe ka kuma babu wanda zai taba tunawa da ka zo duniya.”

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya koka kan halin yunwar da al’umma ke ciki, ya ce abubuwa na kara birkicewa

Bidiyon fitaccen Faston Najeriya yana karanta ayoyin Alkur'ani mai girma

A wani labari na daban, Fasto Tunde Bakare, shugaban cocin Layyer Rain Assembly, ya ba mutane da yawa mamaki yayin da aka gano shi yana karanta wasu ayoyin Alkur'ani a lokacin da yake hira da BBC Yoruba.

A cikin hirar da aka buga a ranar Talata, 3 ga watan Agusta, fasto din da ake girmamawa ya bayyana cewa ya fito ne daga gidan Musulunci mai karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel