Bayan shekara 1 da tunbuke shi, Sanusi II ya fadi abin da ya sa ya zabi ya bar gadon mulki

Bayan shekara 1 da tunbuke shi, Sanusi II ya fadi abin da ya sa ya zabi ya bar gadon mulki

  • Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan rasa rawaninsa
  • Muhammadu Sanusi II ya ce ya hakura da mulki ne domin ya tsira da mutuncinsa
  • Sanusi II ya na ganin babu mamaki an tunbuke shi ne saboda ya na fadin gaskiya

Legas - Mai martaba Malam Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano, ya yi magana a game da tunbuke shi da aka yi daga kan sarautar gidan dabo.

Sahelian Times ta ce yayin da ya yi bikin cika shekara 60, Muhammadu Sanusi II ya yi hira da ‘yan jarida.

Khalifan na darikar Tijjaniya a Najeriya, Malam Muhammadu Sanusi II ya ce da gan-gan da ya hakura da sarautar Kano bayan kusan shekara shida.

Me Sanusi II ya fada game da zargin da gwamnati ta ke yi masa?

“Na nuna adawa ga gwamnatin jiha ta a lokacin da ta nemi ta karbo aron Dala $1.8bn domin aikin jirgin kasa mai daukar mutane, a lokacin da ake da dinbin yara ba su zuwa makaranta, kuma mu na fama da yunwa.”

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya koka kan halin yunwar da al’umma ke ciki, ya ce abubuwa na kara birkicewa

“Na kuma yi kira ayi zaben gaskiya da gaskiya, na ba mutane shawarar su zabi ‘yan takara masu amana da kishi, wadanda za su iya aikin da aka ba su.”
“A wurina, wannan shi ne aikina a matsayin Sarki. Ban san ko wadannan suka jawo aka fara hari na ba, amma na san babu wanda zai wuce kaddara.”

Sanusi II
Muhammadu Sanusi II Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: UGC

“Idan Ubangiji yace lokaci ya yi, magana ta kare.”
“Yin abin da a wuri na ba daidai ba ne, ba zai kara mani kwana daya a gadon sarauta ba. Idan lokaci ya zo, zan bar kan karaga ko a raye, ko a mace.”

Ba za ayi ba daidai ba, in yi shiru

“Watakila kun yi gaskiya domin takardar da aka rubuto mani, ta zarge ni da ‘yi wa gwamnati rashin da’a.’”
“Na zabi in hakura da sarauta domin in tsira da mutunci na, a maimakon in duka wa wani wanda giyar mulki ta dauke shi, da nufin in cigaba da sarauta.”

Kara karanta wannan

Da aka je aka dawo, BOT ta ceci Shugaban PDP daga yunkurin tsige shi, a nada rikon kwarya

Muhammadu Sanusi yake cewa ya saba cewaidan har Sarki zai yi shiru a lokacin da ake yin ba daidai ba, ya zama Bawan da ke daure da rawani a kansa.

Komai yin Allah ne inji Mai martaba

Kwanakin baya Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa a matsayinsa na musulmi, ya yi riko da kaddara, ya ce Ubangiji ne ya ke bada mulki ga duk wanda ya so.

Malam Sanusi II ya ce sarauta rai ne da ita, kuma idan dai an yarda cewa Ubangiji ba ya zalunci sai a gode masa, a maimakon a yi fushi don ya rasa rawaninsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel