Tashin hankali: Dan takarar majalisar wakilai ya yanke jiki ya fadi, ya sheka lahira

Tashin hankali: Dan takarar majalisar wakilai ya yanke jiki ya fadi, ya sheka lahira

  • Allah ya yiwa babban jagaban jam’iyyar PDP dake wuraren Ikare Okomo dake jihar Ondo, Olawale Ogunleye rasuwa
  • Sakataren jam’iyyar, Kennedy Peretei, shine ya tabbatar da rasuwar inda yace ginshikin jam’iyyar ne
  • An samu labarin yadda yaje wani taro a wuraren Ikare Akoko dake jihar kafin aji ya yanke jiki ya fadi a gidansa dake Ikare

Ikare Akoko, Ondo - Sakataren jam’iyyar PDP, Kennedy Peretei, ya sanar da mutuwar jigon jam’iyyar a wuraren Ikare Akoko dake jihar Ondo.

A cewarsa Ogunleye yana daya daga cikin ginshikan jam’iyyar PDP a jihar Ondo saboda ya taba tsayawa a matsayin dan takarar wakilai a mazabar arewa maso gabas da arewa maso yamman Akoko a shekarar 2018.

Tashin hankali: Dan takarar majalisar wakilai ya yanke jiki ya fadi, ya sheka lahira
Tashin hankali: Dan takarar majalisar wakilai ya yanke jiki ya fadi, ya sheka lahira. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito yadda yaje wani taro da aka yi a wuraren Ikare Akoko.

‘Yan uwansa sun yi gaggawar garzayawa dashi wani asibitin kudi a Ikare inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Matasan PDP sun yi wa Jega wankin babban bargo kan kwatanta APC da PDP

A wata takarda wacce sakataren jam’iyyar ya sanya hannu, ya ce mutuwarsa ta bayar da tsoro matuka.

Oluwale ba Najeriya yake zama ba, bai dade da zuwa ba

Kamar yadda Peretei yace:

Oluwale ya iso Najeriya makon da ya gabata daga inda yake zama a Amurka don su yi shagalin zagayowar ranar haihuwar mahaifiyarsa kuma su yi bikin kanwarsa. Har jiya yana nan da rai da lafiyarsa kuma bashi da wata alamar rashin lafiya.

TVC News sun ruwaito yadda Peretei yace Ogunleye ya kai kanshi har asibiti amma nan da mintina kadan ya rasu. Ba bangaren jam’iyyar na Akoko ne kadai suka yi rashi ba, har jihar Ondo ma ta yi asara.

Ya kara da mika ta’aziyyarsa inda yace:

Muna masu baiwa matarsa, yaransa, mahaifiyarsa da kaf ‘yan jam’iyyarmu dake arewa maso gabas ta Akoko hakuri.
Ya taba rike mai baiwa gwamna Olusegun Mimiko shawarwari. Akwai halayensa na ban girma da zamu yi kewa ba kadan ba. Muna yi masa fatan rahama.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Tsohon sanatan Najeriya ya rasu bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya

Miyagun da suka sace yaran Neja sun rage kudin fansa zuwa N50m

Wadanda suka saci yara 2 da manya 7 a Anguwar Kwankwashe a Suleja dake jihar Neja sun bayyana bukatarsu na kudin fansa kimanin naira miliyan 100 zuwa 50.

Daily Trust ta bayyana yadda ‘yan bindigan suka shiga gidajen dake Anguwar Kwankwashe da safiyar Litinin suka yi awon gaba da yara 2 da manya 5.

Wani makusancin ‘yan uwan wadanda aka sace wanda yaso a sakaya sunansa ya ce sai ranar Talata masu garkuwa da mutanen suka kira ‘yanuwanau suna bukatar naira miliyan 100.

Asali: Legit.ng

Online view pixel