Miyagun da suka sace yaran Neja sun rage kudin fansa zuwa N50m

Miyagun da suka sace yaran Neja sun rage kudin fansa zuwa N50m

  • Wasu masu garkuwa da mutane sun saci yara 2 da manya 7 a Jihar Neja sun bukaci naira miliyan 100 zuwa miliyan 50
  • ‘Yan bindigan sun shiga har cikin gidajen da suke Anguwar Kwankwashe a Suleja a ranar Litinin inda suka kwashesu
  • Sai dai wani makusancin ‘yan uwan wadanda aka sace ya bayyana yadda masu garkuwa da mutanen suka kira ranar Talata suna bukatar miliyan 100

Suleja, Niger - Wadanda suka saci yara 2 da manya 7 a Anguwar Kwankwashe a Suleja dake jihar Neja sun bayyana bukatarsu na kudin fansa kimanin naira miliyan 100 zuwa 50.

Daily Trust ta bayyana yadda ‘yan bindigan suka shiga gidajen dake Anguwar Kwankwashe da safiyar Litinin suka yi awon gaba da yara 2 da manya 5.

Miyagun da suka sace yaran Neja sun rage kudin fansa zuwa N50m
Miyagun da suka sace yaran Neja sun rage kudin fansa zuwa N50m. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yaushe miyagun suka tuntubi iyayen yaran?

Wani makusancin ‘yan uwan wadanda aka sace wanda yaso a sakaya sunansa ya ce sai ranar Talata masu garkuwa da mutanen suka kira ‘yanuwanau suna bukatar naira miliyan 100.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane

A cewarsa an cigaba da ciniki dasu daga baya suka rage kudin suka mayar dashi naira miliyan 50, kuma ko a lokacin da yayi bayanin yace akwai jami’an tsaron da suka bi sawunsu.

Bayan an yi ta daga dasu, da kyar suka yarda suka amince da naira miliyan 59 a matsayin kudin fansa duk da dai har yanzu ‘yan uwan suna bukatar a saukar musu da kudin,” a cewarsa.

An yi kokarin tattaunawa da DPO din ofishin ‘yan sanda na Madalla, CSP Adamu Mohammed, amma har lokacin rubuta rahoto ba a same shi ba, Daily Trust ta wallafa.

Daya daga cikin 'yammatan Chibok da mijinta dan Boko Haram sun mika wuya ga sojoji

Tsohuwar dalibar GSS Chibok dake jihar Borno da mijinta, dan Boko Haram sun mika wuyansu ga sojojin Najeriya kamar yadda PRNigeria ta tabbatar.

Dalibar tana daya daga cikin dalibai 200 da ‘yan Boko Haram aka sata a ranar 14 ga watan Afirilun 2014.Duk da dai sojojin basu sanar da sunan dalibar ba, amma an tabbatar da yadda ita da mijinta suka sanar da tubansu daga kungiyar.

Kara karanta wannan

Yan Fashi Sun Kutsa Gidajen Jama'a Sun Yi Awon Gaba da Yara 2 da Wasu da Dama a Neja

An tattaro bayanai akan yadda suka mika wuya kuma suka zubar da makamansu ga dakarun sojin a wani wuri dake kusa da tafkin Chadi.

Wani jami’in binciken sirri ya sanar da PRNigeria cewa akwai wasu ‘yan boko Haram da suka samu sojoji suna nuna yadda suke son su tuba su zubar da makamansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel