Sokoto da sauran jihohin Najeriya guda 5, da yadda sunayensu suka samo asali

Sokoto da sauran jihohin Najeriya guda 5, da yadda sunayensu suka samo asali

Najeriya kasa ce da ba wai kawai ta kunshi wadataccen ma'adinai da albarkatun kasa ba, ta kunshi har ma da albarkatu masu ban mamaki. A al'adun Najeriya, babu sunan da ba shi da ma'ana kama daga sunan mutum har zuwa sunan gari.

Yayin da kowa yasan Najeriya na da jihohi 36 da babban birnin tarayya, ba kowa ne yasan ma'anar sunayen dukkan jihohin ba da kuma yadda suka samo asali.

A cikin wannan rahoton, Legit ta tattaro sunayen wasu jihohi shida da kuma yadda sunayensu suka samu a tarihi.

Sokoto da sauran jihohin Najeriya guda 5, da yadda sunayensu suka samo asali
Wasu jihohi | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

1. Jihar Abia

An samo sunan jihar Abia wacce aka kirkira a shekarar 1991 ta hanyar zabar harafin farko ta Aba, Bende, Isuikwuator, da Afikpo. Abia yanzu ita ce cibiyar kasuwancin jihar tare da Umuahia a matsayin babban birnin jihar.

2. Jihar Oyo

Jihar ta samo sunan ta ne daga masarautar Oyo wacce ta kasance karfin gaske kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Daular tana da mashahuran jarumai wadanda labarin shahararsu ta wuce masarautar.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

3. Jihar Legas

Sunan Legas ya samu ne daga kalmar yaren Fotigal wanda sune Turawan farko da suka fara hulda da birnin. Legas a yaren yana nufin tafki.

4. Jihar Ribas

Sunan jihar ya samu ne duba da yanayin tekun da ke kewaye da shi saboda yankin ya kasance mai ruwa mai yawa. Kalmar Ribas kalma ce ta turanci da ma'anarta koguna.

5. Jihar Sokoto

Duk da cewa Sakkwato siga da aka jirkita daga kalmar Larabci "Suk" wacce take nufin kasuwa, akan kira garin da sunan Sokoto ko Sakkwato, a cewar Hausa Sakkwato birnin Shehu, tunda anan Kalifan muslunci Shehu Usmanu Dan Fodiyo ya zauna.

6. Jihar Kogi

An samo sunan jihar Kogi daga kalmar Hausa Kogi. Shahararren ruwan rudani yana cikin wannan jihar.

Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu

A wani labarin, alakar kudi a matsayin kadarar musaya mai daraja ya ta'allaka da yadda al'umma ke mu'amalantarsu, a Najeriya ma, batun bai sauya zane ba.

Kara karanta wannan

Yan Fashi Sun Kutsa Gidajen Jama'a Sun Yi Awon Gaba da Yara 2 da Wasu da Dama a Neja

Zai baku sha'awa da matukar burgewa ku san yadda ake hada-hada a shekarun da suka gabata a Najeriya ba tare da kudin takarda ko tsaba ko sulalla ba, da kuma yadda lamarin ya sauya zuwa yanzu.

A cikin wannan rahoton, Legit ta tattaro daga Babban Bankin Najeriya abubuwan da ake huldar cinikayya dasu kafin zuwan kudin takarda da sulalla ko tsaba da kuma yadda aka samar da kudaden da muke kashe wa yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel