Yan Fashi Sun Kutsa Gidajen Jama'a Sun Yi Awon Gaba da Yara 2 da Wasu da Dama a Neja
- Wasu yan bindiga sun kutsa gidajen jama'a a Suleja, jihar Neja, inda suka yi awon gaba da mutum 9
- Rahoto ya nuna cewa biyu daga cikin mutanen sun kuɓuta a kan hanyar shigar da su daji
- Jami'an yan sanda sun yi kokarin dakile harin amma saida maharan suka tafi da mutum 7
Suleja, Niger:- Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da kananan yara biyu da wasu mutun bakwai a Anguwar Kwankwashe, Suleja, jihar Neja.
Dailytrust ta ruwaito cewa da farko maharan sun tafi da mutum tara amma daga baya biyu suka kubuta yayin da suke kan hanyar shigar da su daji.
Wani makocin inda lamarin ya faru, Shehu Abdulkadir yace maharan sun shiga yankin da misalin karfe 1:35 na daren ranar Talata.
Ya kara da cewa maharan sun zo da yawansu ɗauke da bindigu kirar AK-47 inda suka kutsa cikin gidajen jama'a da Otal.
Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama
A cewarsa yan bindigan zasu kai akalla mutum 30, wasu daga cikinsu sun sanya kayan sojoji.
Abdulkadir yace:
"Karar harbin bindigarsu ne ya tashe ni daga bacci, na tafi a hankali domin duba abinda ke faruwa ta taga inda na hangi wasu masu garkuwa wasu cikin kayan sojoji."
"Sun shiga wani otal dake yankin, inda suka sace wata mata ɗaya da namiji, yayin da suka cigaba da harbi a sama domin tsorata mutane."
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Wani jami'in tsaron sa kai bijilanti, wanda ya nemi a sakaya sunashi yace ya sanar da ofishin yan sanda dake yankin nan take.
Ya bayyana cewa yan bijilanti sun taimakawa yan sanda inda suka fafata da maharan amma saida suka tsere da mutanen da suka ɗauka.
Da aka tuntubi shugaban caji ofis ɗin Madalla, CSP Adamu Mohammed, ya tabbatar da lamarin amma yaki bada cikakken bayani.
A cewarsa ba shi da ikon fitar da jawabi a hukumance a nemi kakakin hukumar yan sanda na jihar Neja domin karin bayani.
Yan sanda sun ragargaji yan bindiga a Benuwai
A wani rahoton da muka kawo muku kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Kubutar da Matar Kwamishina da Aka Sace
The Nation ta ruwaito cewa yan sanda sun kuɓutar da matar kwamishinan ƙasa, Ann Unenge, a wani operation da suka fita ranar Litinin 2 ga watan Agusta.
Bayan samun nasarar kuɓutar da Unenge, jami'an yan sandan sun tafi da ita hedkwatar rundunar yanda ta jihar.
Asali: Legit.ng