Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

  • Rundunar kwastam ta bayyana yadda ta kame wasu makudan kayayyaki mallakar 'yan bindiga
  • Kayan da aka kame mai darajar miliyoyi an kama su ne a wasu sassan jihar Sokoto a arewacin Najeriya
  • A halin yanzu an mika wadannan kayayyaki ga rundunar hana sha da fataucin miyagu kwayoyi

Sokoto - Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama kunshin tabar wiwi 404 da darajarsu ta kai miliyan 32 a jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kuma kwace wasu haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai Naira miliyan 234 daga shiyyar a zango na biyu na shekarar 2021.

Da yake nuna abubuwan a Sakkwato da Kebbi bi da bi a ranar Laraba, Mataimakin Kwanturola Olurukoba Oseni Aliyu, ya ce sauran kayayyakin da aka kwace sun hada da, shinkafa, jarakunan man fetur, katan din taliya da daurina yadi.

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da ake shigo da 'yan bindiga
Jami'an kwastam na Najeriya | Hoto: dailynigerian.com

Sauran sun hada da magungunan kara kuzarin jima'i, sabbin da tsofaffin takalma, takin NPK, motoci da jarakunan man fetur.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

A cewarsa, tabar wiwi din an tace ta sosai kuma 'yan bindiga na amfani da ita don buguwa.

A cewarsa:

"Wannan shi ne abin da 'yan bindiga ke sha kafin su kai hari tare da kashe 'yan uwanmu."

Kwastan ta gargadi masu fasa kwabri da su daina mummunar dabi'ar

Ya gargadi masu fasa kwabri da su daina wannan mummunar dabi'akuma su goyi bayan gwamnati a kokarin ta na inganta kasa Najeriya.

Ya kara da cewa:

"Gwamnatin mu tana kashe makudan kudade don farfado da tattalin arzikin mu amma wadannan mutanen suna yiwa wannan kokarin zagon kasa."

Ya sake nanata kudirin sa na dakile fasa kwabri a yankin, inda ya ce Kwanturola Janar ya ba da abubuwan da ake bukata don aiwatar da hakan.

A lokacin da yake karbar tabar wiwi da aka kama, wakilin hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta kasa (NDLEA), Mustapha Baba-Ali ya yabawa kwastam kan kamun.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe

NDLEA ta kame wata mata da hodar Iblis kunshe cikin kayanta a filin jirgin sama

Hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta cafke wata mata da ta boye hodar iblis a cikin kayanta a filin jirgin saman Legas, The Cable ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi.

Babafemi ya ce wacce aka kamen mai suna Okafor Ebere Edith an kama ta ne a ranar Asabar 31 ga watan Yuli, lokacin da fasinjoji ke fita daga jirgin saman Cotevoire zuwa Monrovia, Liberia daga filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA), Ikeja, Legas.

NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta

A wani labarin, Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Brazil, Misis Anita Ugochinyere Ogbonna, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA) dake Abuja, dauke da kwalayen hodar iblis 100 da ta boye a al'aurarta da jakarta.

Kara karanta wannan

Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fada a ranar Lahadi a Abuja cewa an kama matar mai 'ya'ya uku ne a daren Juma’a lokacin da suka isa Abuja ta jirgin Qatar Air daga Sao Paulo na Brazil ta Doha babban birnin kasar Qatar.

A cewarsa, yayin binciken kwakwaf, an ciro hodar iblis 12 da ta saka a al'aurarta yayin da aka gano wasu kunshi 88 da aka saka a cikin safa a boye cikin jakarta, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel