Falana: Janar Buratai ya so kasar Benin ta damka masa Igboho a hannunsa, sai aka kunyata shi

Falana: Janar Buratai ya so kasar Benin ta damka masa Igboho a hannunsa, sai aka kunyata shi

  • Gwamnatin Najeriya ta yi yunkurin dauko Sunday Igboho daga Jamhuriyyar benin
  • Kasar Benin ce ba ta yarda da wannan bukata da Jakadan Najeriya ya gabatar ba
  • Femi Falana ya ce sabon Jakadan Najeriya zuwa Benin, Buratai ne ya nemi hakan

Abuja - Babban lauya mai kare hakkin Bil Adama a Najeriya, Femi Falana, ya yi ikirari Tukur Yusuf Buratai ya nemi Benin ta damka masa Sunday Igboho.

Jaridar The Cable ta rahoto Femi Falana SAN ya na cewa gwamnatin Benin ba ta amince da bukatar Jakadan na Najeriya ba, ta ce a bar doka ta yi halinta.

Da yake magana a kan shari’ar Sunday Igboho wanda yake tsare a Benin tun ranar 19 ga watan Yuli, 2021, a Channels TV, Falana ya bayyana abin da ya faru.

Da yake jawabi a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, 2021, Falana ya ce Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya roki gwamnatin Benin ta mika masa Cif Igboho.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

A cewar fitaccen lauya, Jakadan Najeriyar ya tanadi wani jirgin sama domin a dawo da Igboho daga Benin, da nufin a zartar masa da hukunci a kotun gida.

“A lamarin Sunday Igboho, a nan ma akwai sabani tsakani na da su, na fito ina cewa ba zai yiwu kawai ka tura mutum a cikin jirgi ba, an yi yunkurin yin haka.”

Femi Falana
Babban Lauya, Femi Falana SAN
Asali: UGC

“Dole ka je kotu, ka mika bukata a karkashin dokokin kasar waje, kamar yadda ECOWAS ta tanada.”
“Gwamnatin Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar Benin ta mika mata Sunday Igbojo, a lokacin Janar Yusuf Buratai (rtd) bai gabatar da takardun jakadanci ba.”
“Sai aka fada masu cewa, ‘ku yi hakuri, mu na aiki da doka a nan’, shiyasa har yanzu batun na kotu.”

Gawurtaccen lauyan yake cewa muddin mutanen Najeriya ba su bin dokoki tare da tsare hakkin Bil Adama, za a cigaba da ba mu kunya a idanun kasashen Duniya.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na tsere daga Najeriya, na zo Benin – Igboho ya yi bayanin komai a kotu

Sabon Jakadan Najeriya ya taka rawar gani wajen cafke Igboho

Laftana Janar Buratai mai ritaya ya rike mukamin hafsun sojojin kasa tsakanin 2015 da 2021. Daga baya aka nada shi matsayin Jakada zuwa Jamhuriyyar Benin.

Rahotanni sun nuna Tukur Buratai ya taimaka wajen cafke Sunday Igboho a Cotonou. Sabon Jakadan Najeriyan ya rubuta takarda, ya sanar da kasar a kan Igboho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel