Dalilin da ya sa na tsere daga Najeriya, na zo Benin – Igboho ya yi bayanin komai a kotu
- Lauyan Sunday Adeyemo ya bayyana yadda shari’arsa ta ke gudana a Benin
- Ibrahim Salami ya ce Igboho ya yi wa Alkali bayanin abin ya sa ake nemansa
Sunday Igboho ya fada wa Alkali cewa bai taba yin laifin komai a Najeriya ba
Ban yi laifin komai a Najeriya - Sunday Adeyemo
Benin - Sunday Adeyemo wanda mutane suka fi sani da Sunday Igboho, ya musanya zargin da gwamnatin Najeriya ta lafta a kansa na kama shi da makamai.
Jaridar Punch ta rahoto Sunday Adeyemo ya na cewa zargin samunsa da laifin safarar makamai ko yunkurin tada zaune tsaye a Najeriya, sam ba gaskiya ba ne.
Babban lauyan da yake kare wannan mutum, Ibrahim Salami, ya yi hira da BBC Yoruba a ranar Talata.
Ibrahim Salami ya shaida wa manema labarai abin da Sunday Igboho ya fada wa Alkalin da ke sauraron shari’arsa a garin Cotonou, jamhuriyyar kasar Benin.
Lauyan ya ce ana tuhumar Igboho ne da sababbin laifuffuka da suka hada da haramtaciyyar hijira, da kuma hada kai da jami’an shige da fice wajen shirya ta’asa.
Har ila yau ana zargin Sunday Igboho da yunkurin tada zaune tsaye a babban kotun na kasar Benin.
“Da Alkali ya tambayi Cif Sunday Adeyemo ya yi bayani a kan laifuffukan da ake zargin sa da aikata wa, sai ya ce bai yi wani abin da ya saba doka a gida ba.”
“Ya yi karin-haske cewa Najeriya ba ta taba kai shi kotu da sunan ya yi laifi ba, ba a taba kama shi ana zarginsa da laifi, ko ‘yan sanda suka gayyace sa ofis ba.”
“Igboho ya fada wa Alkali cewa gwamnatin tarayya ta na neman shi ne saboda ya na kare kabilar Yarbawa daga miyagun makiyaya Fulani da ke kashe Bayin Allah.”
Ya ce ya tsere daga Najeriya ne saboda gwamnati na neman ganin bayansa. Alkali ya yarda Igboho bai yi laifi a Benin ba, sai dai kurum za a binciki yadda ya shigo.
Sarkin Fulani Ya Yi Magana Kan Shari'ar Igboho a Benin, Ya Bukaci Gwamnati Ta Taso Keyar Shi Zuwa Najeriya
"Igboho ya ce ya bar Najeriya ne a ranar Lahadi ya zo kasar Benin, da niyyar zuwa Jamus a ranar Litinin da dare, sai aka cafke shi."
Asali: Legit.ng