Da Haɗin Bakin Birtaniya Aka Jefa Nnamdi Kanu Cikin Halin Da Ya Shiga, Lauyansa

Da Haɗin Bakin Birtaniya Aka Jefa Nnamdi Kanu Cikin Halin Da Ya Shiga, Lauyansa

  • Daya daga cikin lauyoyin da ke kare Nnamdi Kanu ya yi ikirarin cewa Birtaniya na da hannu cikin ukubar da shugaban na IPOB ke ciki
  • Lauyan mai suna Ifeanyi Ejiofor ya yi wannan zargin ne a yayin da ake tattaunawa da shi a wani shirin talabijin a ranar Laraba
  • Ejiofor ya yi ikirarin cewa gwamnatin na Birtaniya bata bawa Nnamdi Kanu irin taimakon da ya ke bukata ba duk da cewa shi dan kasarta ne

Ifeanyi Ejiofor, daya daga cikin lauyoyin da ke kare shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya yi zargin cewa akwai yiwuwar gwamnatin Birtaniya na da hannu cikin jefa wanda ya ke karewa halin da ya shiga, rahoton The Punch.

The Punch ta ruwaito cewa Ejiofor ya yi wannan zargin ne a ranar Laraba yayin wani shiri da aka yi da safe a gidan Talabijin na Arise.

Da Haɗin Bakin Birtaniya Aka Jefa Nnamdi Kanu Cikin Halin Da Ya Shiga, Lauyansa
Shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Na tabbata da hannun Birtaniya cikin halin da Nnamdi Kanu ya shiga, Lauyansa

Ya yi zargin cewa akwai hadin baki da gwamnatin kasar Birtaniya.

Ejiofor ya ce:

"Ina tabbatar maka da cewa gwamnatin Birtaniya bata yin abin da ya dace don taimakonsa kan lamarin. Ina tabbatar maka akwai yiwuwar hadin bakinsu kan abin da ya ke faruwa da wanda na ke karewa.
"Saboda a shekarar 2015 lokacin da aka kama wanda na ke karewa, na san yadda suka rika tuntubarsa tare da kai masa ziyara, a lokacin yana hannun sojoji da lokacin da ya ke hannun DSS da ma gidan yari.
"A lokacin da aka kama shi, shi dan Birtaniya ne domin ya yi hannun riga da Nigeria a matsayin kasarsa tun shekaru biyar da suka shude. Kuma har yanzu suna batun bashi taimako daga ofishin jakadanci."

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A wani labarin, shugaban na haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel