Kotu Ta Yi Watsi da Wata Bukatar Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

Kotu Ta Yi Watsi da Wata Bukatar Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

  • Kotu taki amincewa da bukatar Nnamdi Kanu, na ɗauke shi daga hannun DSS zuwa gidan Yari
  • Mai shari'a Binta Nyako, ta bayyana cewa ba zata amince da wannan bukatar ba, a ofishin DSS za'a cigaba da tsare shi
  • Saboda rashin kawo Kanu kotu, Nyako ta bayyana ɗage sauraron ƙarar har zuwa watan Octoba

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da bukatar Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar yan aware IPOB, da ya nemi a ɗauke shi daga hannun DSS zuwa gidan yarin Kuje, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Shugaban majalisar lauyoyin Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor, shine ya gabatar da buƙatar wanda yake karewa a ranar Litinin, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Nnamdi Kanu ya kasance a hannun jami'an tsaron farin kaya DSS tun bayan da aka sake kame shi a kasar waje kuma aka dawo da shi Najeriya, yana fuskantar shari'a kan cin amanar ƙasa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu

Nnamdi Kanu
Kotu Ta Yi Watsi da Wata Bukatar Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

A bukatar Kanu, ya bayyana cewa "Ana azabtar da shi ta kowane fanni" a hannun DSS, kuma yayi korafin cewa an hana shi ganin likitocinsa.

Ejiorfor, ya nuna rashin jin daɗinsa da rashin gurfanar da Kanu a yau Litinin kamar yadda aka tsara.

Lauyan ya yi zargin cewa ana azabtar da wanda yake karewa matuƙa kuma ba'a bashi damar gana wa da lauyoyinsa yanda ya kamata yayin da yake hannun DSS.

Mai shari'a Nyako ta yi watsi da bukatar

Sai dai mai jagorantar shariar, Alkali Binta Nyako, ta yi watsi da buƙatar da wanda ake zargi ya nema.

Nyako ta ƙara da cewa zata bada umarnin a bar Lauyoyinsa suna ganinsa a lokutan da ya dace.

A Jawabin Nyako, tace: "A'a ba zan bada umarnin a maida shi gidan yari ba, jami'an DSS zasu cigaba da tsare shi, amma zan bada umarnin a baku dama kuna ganinshi."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Kasuwa Sun Garkame Shagunansu a Aba Saboda Shari'ar Nnamdi Kanu

"Amma ba kowa za'a bari yana zuwa ganinsa ba, ganin nasa zai kasance a tsare. Domin bazai yuwu ka taso da daddare kace kanason ganawa da shi ba."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sake Aikewa da Sako Ga Iyayen Daliban Bethel Baptist Kaduna

Shugaban yan Baptist reshen jihar Kaduna, Ishaya Jangado, yace za'a sako ragowar daliban makarantar Bethel Baptist kashi-kashi.

Adadin ɗalibai 121 ne aƙa sace lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari makarantar ranar biyar ga watan Yuli.

Da farko ɓarayin sun sako ɗalibi ɗaya saboda matsalar da ta shafi lafiya yayin da jami'an yan sanda suka kuɓutar da wasu guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262