Jerin sabbin manyan laifuka 3 da jamhuriyar Benin ke tuhumar Sunday Igboho akai

Jerin sabbin manyan laifuka 3 da jamhuriyar Benin ke tuhumar Sunday Igboho akai

  • Jamuriyar Benin ta tsare Sunday Igboho tare da cewa, tana zarginsa da sabbin laifuka da ta gano
  • Legit Hausa ta tattaro laifukan guda uku da gwamnatin Benin ta ce tana zargin Sunday Igboho akai
  • A baya, Sunday Igboho ya tsere daga Najeriya yayin da ya yi kokarin zillewa zuwa Jamus ta Benin

Ibrahim Salami, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Igboho ya bayyana cewa an bijiro da sabbin tuhume-tuhume a kan Sunday Igboho a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, yayin zaman kotu, jaridar The Punch ta ruwaito.

Wadannan su ne uku daga cikin manyan laifukan da gwamnatin jamhuriyar Benin ke tuhumar Igboho akai:

  1. Hijira ba bisa ka'ida ba
  2. Hadin baki da jami'an shige da fice
  3. Kokarin haifar da tarzoma
Jerin manyan laifukan da jamhuriyar Benin ke tuhumar Sunday Igboho akai
Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa | Hoto: saharareporters.com
Asali: Facebook

Kotun ta yanke hukuncin cewa Igboho zai ci gaba da kasancewa a tsare yayin da hukumomin jamhuriyar Benin suke bincikar sabbin zarge-zargen da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Hatta Musa Ya Yi Hijira Saboda Fir'auna, Babu Laifi Don Igboho Ya Tsere, Afenifere

Dangane da zargin, Salami ya ce idan da Igboho yana son haifar da rikici a Benin kamar yadda ake zargi, da zai dade a kasar, amma a shirye yake ya bar kasar cikin kasa da awanni 24 da isowarsa, inji rahoton The Cable.

Salami ya ce zarge-zargen da suka gabata da suka bayar da damar sanya Igboho cikin jerin masu sa ido an yi nasarar magance su yayin sauraren karar.

Wasu daga cikin zarge-zargen, wadanda ya ce ba za a iya tabbatar da su ba; fataucin makamai ne, da iza wutar rikici da ka iya haifar da rudani a cikin al’umma da haifar da rabuwar kai a Najeriya.

Lauyan ya ce kungiyar lauyoyin sun yi tsammanin cewa za a saki Igboho a ranar Litinin saboda har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta gabatar da tuhumar tasa keyarsa ba.

Shari'ar, ta dauki sabon salo domin yanzu ta zama tsakanin Jamhuriyar Benin da Igboho.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Me yasa Igboho ya bar Najeriya?

Makonni kadan da suka gabata, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta mamaye gidan Igboho da ke Ibadan bayan ta zarge shi da tara makamai.

Mamayar ta kai ga kashe wasu mutane biyu na Igboho amma dan awaren Yarbawan ya tsere.

Daga baya ne DSS ta bayyana cewa ana neman Igboho.

An kama Igboho a ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, a tashar jirgin sama ta Cotonou, Jamhuriyar Benin a kan hanyarsa ta zuwa Jamus.

Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

A wani labarin, Sarakunan Yarbawa a Jamhuriyar Benin, a ranar Lahadi, sun gana a kan kamawa da tsare dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

An yi taron ne a Fadar Alajohoun na Adjohoun, wanda ke da tazarar kusan kilomita 60 daga Ajase.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Alajashe na Ajase daga Port Novo, Alajohoun na Adjohoun, Onikoyi Abesan, da Oba na Seme.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.