Cikin Hotuna: Daliba ta kammala jami'a da sakamako mai kyau, ta ci lambobin yabo da dama

Cikin Hotuna: Daliba ta kammala jami'a da sakamako mai kyau, ta ci lambobin yabo da dama

  • An tura wata matashiya ‘yar Najeriya, Ismail Aminat cikin Kwalejin Kimiyya ta Najeriya bayan kammala karatunta da digiri mafi daraja
  • Matashiyar ta samu kyaututtuka da yawa bayan ta zama zakara a cikin daliban da suka kammala karatun digiri a fannin Kimiyyar gwaje-gwaje a jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola
  • Aminat ta wallafa kyawawan hotunanta don nuna farin cikinta inda 'yan Najeriya suka mamaye sashenta na sharhi da sakonnin taya murna

Wata matashiya 'yar Najeriya mai suna Ismail Aminat tayi murnar nasarorin da ta samu a bangaren ilimi bayan ta zama dalibar da ta fi kowa kokari a fannin kimiyar gwaje-gwaje (2019/2020) a Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola.

Matashiyar ta je shafin soshiyal midiya domin murnar nasarar da ta samu, inda ta ce an tura ta Cibiyar Nazarin Kimiyyar Gwaje-gwaje ta Najeriya (NISLT).

Matashiya ta yi bikin zamowarta daliba mafi kwazo, ta samu kyaututtuka da dama
Ismail Aminat ta yi farin ciki da nasarorin da ta samu Hoto: Ismail Aminat
Asali: Facebook

Aminat, wacce ta kammala karatunta da digiri mafi daraja (4.71 / 5.00), ta sami lambobin yabo da yawa saboda kwarewarta a fannin karatu.

Kara karanta wannan

Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya

Kyaututtukan da yarinyar ta karɓa

Da take wallafa kyawawan hotuna a shafinta na Facebook, Aminat ta jera kyaututtukan da ta samu na zama zakara a ajinta.

A kalamanta:

“1. Dalibar da ta kammala da digiri mafi daraja a Chemistry/Biochemistry Option ajin 2019/2020. 2. Daliba mafi kokari a fannin Chemistry/Biochemistry Option ajin 2019/2020. 3. Dalibar da ta fi kowani dalibi kokari SLT ajin 2019/2020. Ya kasance tare da farin ciki na sami lambar yabo ta Palmaris’19; 1. Daliba mafi kokari ta shekara. 2. Kyautar bangirma a fannin ilimi.

Aminat tana godiya

Matashiyar ta nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki, iyayenta da masoyanta bisa gudummawar da suka bayar don nasararta.

Aminat tayi ma kanta fatan alkhairi sosai kamar yadda ta nuna a shirye take don samun nasara a gaba.

Masu fatan alheri sun taya budurwar murna

Okunoye Adenike Ojuolape ya ce:

"Ina taya ki murna, ina alfahari da ke, Allah ya kara daukaka, Allah ba zai bar ki ba Ijn."

Kara karanta wannan

Kanu da Igboho: Kungiyar arewa ta dau zafi, ta bayyana abun da ya kamata FG ta yi wa ‘yan bindiga da makiyaya

Maryam Mustapha Bello ta yi tsokaci:

"Ina taya ki murna ya yar’uwa. Barakallahufih. Ya ‘yan LADOKITE ina alfahari da ke ..."

Alubarika Asiwaju Farms ya rubuta:

"Madalla! Kin cancanta!"

Kazeem Abiobun Olatunde ya ce:

"Wannan abin birgewa ne! Ina taya ki murna!"

Kyakkyawar budurwa ta ciri Tuta a jami'ar jihar Gombe, ta karya tarihi

A gefe guda, wata 'yar Najeriya, Halima Yayajo, ta samu gagarumin nasara a jami'ar jihar Gombe, inda ta zama zakarar shekara a fannin ilmin Likitanci.

Wata mai suna Fadilat Idris, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook inda ta daura hotunan lambobin yabon da Halima ta samu da kuma hoton bikin yayesu.

Halima ta samu lambobin yabo guda tara a fannoni daban-daban na karatun koyon Likitanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel