Kanu da Igboho: Kungiyar arewa ta dau zafi, ta bayyana abun da ya kamata FG ta yi wa ‘yan bindiga da makiyaya
- Wata fitacciyar kungiyar Kudancin Kaduna, SOKAPU, ta nemi gwamnatin tarayya da ta bayyana ‘yan fashi da makiyaya makasa a matsayin ‘yan ta’adda
- Shugaban kungiyar SOKAPU, Jonathan Asake, ya ce dole ne gwamnati ta sa kafar wando daya da 'yan fashi kamar yadda ta ke yi da masu tayar da kayar baya a kudu
- Asake ya bayyana cewa 'yan bindigar sun ma fi hadari ga hadin kan Najeriya fiye da masu son ballewa dagwamnatin ta ke amfani da dukkan karfinta wajen yakarsu
Kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda take rikon lamarin ‘yan fashi da makiyaya da ke addabar yankin arewacin kasar.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta arewa ta bukaci gwamnati da ta yi amfani da irin dabarun da aka bi wajen kamo shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, da kuma dan rajin kare kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda ake kira Sunday Igboho, wajen magance matsalar. 'yan fashi.
Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kungiyar SOKAPU na kasa, Jonathan Asake, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli.
'Yan fashi sun fi zama barazana ga hadin kan Najeriya fiye da masu son ballewa
Asake ya bukaci gwamnati da ta daina lallaba ‘yan fashi da makami a arewacin kasar, yana mai lura da cewa ayyukansu na barazana ga hadin kan Najeriya fiye da masu neman ballewa.
Da yake ci gaba da magana, Asake ya ce kungiyar ta gamsu ba tare da wata shakka ba cewa gwamnati na da karfin da za ta iya yaki da barayi wadanda suka sanya rayuwar ‘yan kasa cikin wani yanayi.
Ya ce yadda gwamnatin tarayya ta ke maganin ‘yan bindigar Benuwai, Terwase Akwaza, aka Gana, Kanu, Igboho da sauransu ya nuna cewa tana da isasshen karfin da za ta yi maganin ‘yan fashin.
Kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da rashin nuna matakan da suka dace na tunkarar ‘yan fashin ko da bayan wasun su sun harbi wani jirgin sama a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli.
A ayyana ‘yan bindiga, makasan makiyaya a matsayin yan ta’adda
SOKAPU ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta hanzarta bayyana ‘yan fashi da makami da masu satar mutane a matsayin ‘yan ta’adda.
A cewar Asake, ayyukan 'yan ta'addan sun jefa mutane cikin wani mawuyacin hali tare da lalata gonaki, jaridar Leadership ta ruwaito.
Ya ce:
"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta ayyana wadannan Fulani makiyaya masu dauke da makamai, masu satar mutane da 'yan fashi a matsayin 'yan ta'adda."
A wani labarin kuma, wata kungiya mai suna 'Africa's New Dawn' ta bukaci ɗan gwagwarmayar Yarbawa, Sunday Igboho da Nnamdi Kani, shugaba IPOB su yi watsi da gwagwarmayarsu su fito takarar shugaban kasa a 2023, rahoton The Guardian.
Shugaban kungiyar na kasa, Iluckukwu Chima, yayin da ya ke sanar da taron wayar da kan mutane da za su yi mai taken, 'One Love, One Nation, One President', a ranar Alhamis a Abuja ya ce zaman Nigeria a matsayin ƙasa guda ya fi alheri ga kowa.
Yayin da gwamnatin Nigeriya ke tsare da Kanu, Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho yana hannun jami'an tsaro a Jamhuriyar Benin bayan kama shi a filin tashin jirage na Bernardin tare da matarsa a hanyarsu na zuwa Jamus a daren ranar Litinin.
Asali: Legit.ng