Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya

Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya

  • Matar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Chief Mbazulike Amechi ta kwanta dama
  • Tsohuwar ma'aikaciyar jinyar ta rasu tana da shekaru casa'in a duniya
  • Mbazulike ya yi alhinin mutuwar matarsa wacce yace ta raine shi duk da ayyukanta

Nnewi, Anambra - Iyom Chinelo, matar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Chief Mbazulike Amechi ta rasu, Daily Trust ta wallafa.

Amechi ta rasu ne a ranar 23 ga watan Yulin 2021 a asibitin koyarwa na jami'ar Nnamdi Azikiwe dake Nnewi bayan kwashe kwanaki goma da tayi tana jinya.

'Yar asalin Umuoji dake karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar, marigayiyar ta yi murabus daga aikinta na shugabar ma'aikatan jinya a shekarar 1982 daga babban asibitin Mburi dake Nnewi wanda yanzu ake kira da NAUTH.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC

Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya
Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ubangiji ya juyawa Buhari baya, Fasto Bakare ya bayyana a sabon bidiyo

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan daba suka kai masa farmaki

Tsohon minista yayi alhinin mutuwar matarsa

Mbazulike wanda ya zanta da manema labarai a ranar Talata a gidansu dake Ukpor, karamar hukumar Nnewi ta kudu dake jihar, ya kwatanta marigayiyar matarsa da kwararriyar ma'aikaciyar jinya kuma mace tagari wacce ta iya aikinta tare da kula da gida.

Kamar yadda yace, shekarun da suka diba da matarsa masu matukar dadi ne kuma dole dukkan iyalan su yi kewarta, Daily Trust ta wallafa.

"Kwararriyar ma'aikaciyar jinya ce kuma mace tagari. Ta iya hada aikinta da ayyukan gidanta.

"Ina farin cikin aurenta da nayi saboda ta taimaka wurin raino na. Ita ce shugabar kungiyar matan katolika a coci. Ta taka rawar gani yayin da nake gwagwarmayar aiki da kasa," yace.

Soyayyar wata goma muka yi kafin aure

A yayin da ya kwatanta kansa da Kiristan gargajiya wanda ya tsani tara mata, dattijon ya ce ya sha alwashin ba zai yi aure ba har sai Najeriya ta samu 'yancin kanta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu

Ya ce daga bisani ya aureta bayan kwashe watanni goma da suka yi suna soyayya. Mamaciyar ta rasu tana da shekaru casa'in da daya a duniya

An sace sojojin Najeriya biyu a Borno

A wani labari na daban, jami'an rundunar sojin kasa na Najeriya guda biyu, Bello Abubakar da Oyediran Adedotun sun shiga hannun 'yan bindiga a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a yankin Goni Masari dake Borno.

Sojojin da aka yi garkuwa dasu suna kan hanyarsu ta zuwa Kano ne a wata motar farar hula wurin karfe 5 na yammacin ranar Asabar, kamar yadda sakon birged ta 29 ya nuna kuma SaharaReporters ta ruwaito.

An gano cewa fasinjojin dake cikin motar sun zargi direban yana da alaka da 'yan bindigan, lamarin da yasa fasinjojin suka sanar da sojojin dake sansanin Mainok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel