Daga Yanzu, Wajibi Ne Kowane Dalibin Sakandire a Kano Ya Mallaki NIN, Gwamnatin Ganduje

Daga Yanzu, Wajibi Ne Kowane Dalibin Sakandire a Kano Ya Mallaki NIN, Gwamnatin Ganduje

  • Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa ya zama wajibi kowane dalibin sakandire a jihar ya yi rijistar NIN
  • Kwamishinan Ilimi, Muhammad Sanusi, yace mallakar NIN zai taimakawa gwamnati wajen samun sahihin bayanan dalibai
  • A cewaesa, wannan mataki zai dakatar da canza bayanan dalibai yayin jarabawa da rage satar amsa

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa ya zama wajibi dukkan ɗaliban sakandiren jihar su yi rijista kuma su mallaki lambar zama ɗan kasa NIN, tun daga karamar sakandire JSS zuwa babba SS, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kwamishinan ilimin jihar, Muhammad Sanusi Kiru, shine ya bada sanarwar yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne domin gwamnati ta samu cikakken bayanan dalibai kuma hakan zai saukaka wajen yin kasafi da sauran lamarin da ya shafi dalibai, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Lamabar katin ɗan kasa, NIN
Daga Yanzu, Wajibi Ne Kowane Dalibin Sakandire a Kano Ya Mallaki NIN, Gwamnatin Ganduje Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Kiru Ya ƙara da cewa idan ɗalibai suka yi rijista kuma suka mallaki NIN zamu samu damar samun bayanan halittarsu, zanen yatsu 10, karamin hoton ɗalibi, da kuma sanya hannun kowane ɗalibi.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Hakazalika yace hakan zai taimaka wajen dakatar da yawan canza bayanan ɗalibai yayin jarabawa da kuma rage damar satar amsa a jarabawa

Muna bukatar aiwatar da hakan nan take

Kwamishinan ya yi kira ga shugabannin hukumar makarantu, (KSSMB), daraktoci, shugabannin sakandire da su tabbatar an aiwatar da wannan sabon umarni.

Yace: "Ma'aikatar ilimi ta kammala duk wasu shirye-shirye tare da ofishin hukumar NIMC na jihar Kano game da yadda za'a yiwa ɗaliban rijistan a yankunansu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262