2023: Kungiyoyin matasan arewa sun ce bukatar kudu na neman a mika masu mulki laifi ne

2023: Kungiyoyin matasan arewa sun ce bukatar kudu na neman a mika masu mulki laifi ne

  • Kungiyoyin matasan Arewa sun ce bukatar da kungiyar Gwamnonin Kudancin kasar nan ta nema na mika mulki a 2023 abin takaici ne
  • Kungiyoyin sun bayyana cewa bukatun sun nuna cewa gwamnonin kudu basu da kwarewa a al'amuran siyasa
  • Muhawara kan ko mulki ya koma kudancin Najeriya ko ya ci gaba da zama a arewa na ta wakana tsawon wasu yan watanni

Jimlar kungiyoyin matasan arewa guda arba’in da biyu (42) a karkashin inuwar kungiyar shugabannin matasan Arewa (NYLF) sun bayyana bukatar gwamnonin kudu na neman mika shugabancin kasa ga kudu a 2023 a matsayin rashin tunani, cin fuska, da kuma tsokana.

Shugaban NYLF na kasa, Eliot Afiyo, wanda ya bayyana matsayin kungiyoyin a taron manema labarai a Yola, jihar Adamawa, ya ce gwamnonin kudu sun fallasa rashin gogewarsu da yarintarsu a siyasa da irin wadannan bukatun.

KU KARANTA KUMA: "Ka kiyaye ni," Gwamnan Zamfara ya gargadi mataimakinsa

Kara karanta wannan

2023: Cancanta za mu duba wajen zabar Shugaban kasa, kungiya ta bayyana zabinta

2023: Kungiyoyin matasan arewa sun ce bukatar kudu na neman a mika masu mulki laifi ne
Matasan arewan na martani ne ga buktar gwamnonin kudu na baya-bayan nan Hoto: Lagos state government
Asali: Facebook

Afiyo ya ci gaba da cewa sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnonin kudu ba su da kwarewar siyasa da tsari.

Jaridar Nigerian Tribune ta nakalto yana cewa:

"Mun dauki wannan furucin a matsayin mai tayar da hankali, rashin tunani, cin fuska, kalubale da kuma ayyana yakin siyasa wanda dole ne a ba shi cikakken tunani da aiki."

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

2023: Cancanta za mu duba wajen zabar Shugaban kasa, kungiya ta bayyana zabinta

A gefe guda, wata kungiya mai suna National First Movement, ta nuna goyon bayanta ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya ce mulkin karba-karba ya saba wa kundin tsarin mulki.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa cancanta da karfin isar da aiki su ya kamata su mamaye sararin siyasarmu yayin da 2023 ke gabatowa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu

Ta gargadi masu ruwa da tsaki a kasar da su fifita cancanta da kwarewa yayin da zabukan 2023 ke gabatowa don magance dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel