2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu

2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu

  • Rahotanni sun kawo cewa ‘yan majalisar dokokin jihohin Arewa sun ce ya kamata arewa ta sake samar da wanda zai gaji Shugaba Buhari a 2023
  • A cewar 'yan majalisar, yankin kudu ya yi mulki na shekaru 14 yayin da arewa za ta yi shekaru 10 kawai lokacin da Buhari ya gama wa’adinsa a 2023
  • 'Yan majalisar sun kuma goyi bayan kudirin Yahaya Bello na takarar shugaban kasa, suna masu cewa gwamnan na Kogi yana da duk abin da ake bukata don mulkar Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan majalisar dokokin jihohin Arewa sun ce arewa ta cancanci ci gaba da rike shugabancin kasar bayan ficewar Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

‘Yan majalisar sun yi jayayya a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, cewa yankin kudu ya yi mulki na shekaru 14 yayin da arewa za ta yi mulki na shekaru 10 a karshen mulkin Shugaba Buhari, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

KU KARANTA KUMA: Gwamnan PDP ya caccaki majalisar dattawa, ya ce mika ikon INEC ga NCC ya saba wa kundin tsarin mulki

2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu
Yan majalisun arewa sun nuna goyon bayansu ga takarar Gwamna Yahaya Bello na Kogi Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa sun taru ne a Abuja a kan kudirin neman takarar gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a 2023.

Sun roki gwamnan na Kogi da ya tsaurara tuntube-tuntubensa don darewa babban kujerar siyasar kasar.

Taron ya samu halartar wakilai hudu daga dukkan jihohin da ke yankin arewacin kasar.

Ku goyi bayan takarar Bello a 2023 - Kakakin Kogi

Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi kuma wanda ya jagoranci taron, Matthew Kolawole, ya yi kira ga mahalarta taron da su goyi bayan kudirin Gwamna Bello na neman shugabancin kasar, jaridar The Cable ta ruwaito.

Ya yi magana game da karfin kuzari da kuma kwarewar da gwamnan Kogi yake da shi, yana mai cewa ana bukatar su don ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Muhuyi Rimingado

An bukaci 'yan majalisar da su fara ba da shawara tare da tuntubar wadanda suka zabe su da masu ruwa da tsaki kan burin Gwamna Bello.

KU KARANTA KUMA: Dokar Zabe: Ƴan Majalisar PDP Sun Harzuka, Sun Fice Daga Zauren Majalisa a Fusace

Leadership ta ruwaito cewa dukkansu sun yanke hukuncin cewa Gwamna Yahaya Bello "ya cancanta kuma yana da kwarewar da ake bukata don hawa kujerar."

Shugaban kasa a 2023: Kungiyar Arewa ta yiwa Ohanaeze wankin babban bargo kan furucinta game da Yahaya Bello

A gefe guda, kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYFC) ta caccaki kungiyar Ohaneaze saboda ta amince da "tsarin da ake kira mulkin karba-karba" gabanin babban zaben 2023.

Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, kuma Legit.ng ta gani, ta lura cewa babu inda za a iya samun tsarin mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Dangane da kin amincewa da matsayin Gwamna Yahaya Bello kan shugabancin karba-karba da Ohaneaze ta yi, AYCF ta bayyana takamar kungiyar a matsayin mara amfani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng