Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

  • ‘Yan bindiga da ke biyayya ga Turji, wani mashahurin dan ta’adda sun kai farmaki kauyuka da yawa a cikin karamar hukumar Shinkafi
  • An ce 'yan fashin da suka yi garkuwa da mutane kimanin 150 sun dauki matakin ne bayan kamun mahaifin Turji
  • An tattaro cewa Turji ya nuna bacin ransa game da kamun mahaifinsa, yana mai cewa shi ne wanda ya kamata jami'an tsaro su bi musamman ganin cewa wurisa ba boyayyen wuri bane

‘Yan bindiga da ke biyayya ga wani fitaccen dan fashi a jihar Zamfara, da aka fi sani da Turji, suna ta yin dirar mikiya, suna garkuwa da mutanen gari da matafiya a karamar hukumar Shinkafi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Jaridar ta kara da cewa matakin da 'yan bindigar suka dauka ya biyo bayan kama mahaifin Turji da aka yi kwanan nan.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a Katsina

Kara karanta wannan

Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya fatattaki kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa
Turji ya kai hare-hare kauyukan Zamfara inda ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa Hoto: Governor Bello Matawalle
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa hare-haren sun fara ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli, kuma sunci gaba inda aka yi garkuwa da kimanin mutane 150.

An rahoto cewa jami’an tsaron sun kama mahaifin Turji a cikin garin Kano kimanin makonni biyu da suka gabata kuma tun daga nan ba a san inda yake ba.

KU KARANTA KUMA: Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum

Kauyukan da aka kai hari ranar Juma’a:

1. Kurya

2. Keta

3. Kware

4. Badarawa

5. Marisuwa

6. Maberaya, da sauransu

Baya ga fatattakar kauyukan, an rahoto cewa yan bindigan sun kuma sace matafiya da yawa akan hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Turji ya lashi takobin hana mutane da yawa jin daɗin Sallah tare da danginsu

An yi zargin cewa Turji ya sha alwashin cewa idan har za a hana mahaifinsa yin Sallah mai zuwa a gida to zai kuma tabbatar da cewa wasu mutane da yawa ba su yi bikin tare da danginsu ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro a Igangan

Daily Trust ta nakalto wata majiya tana cewa Turji ya yi tir da kamun mahaifinsa. Shugaban 'yan fashin ya ce shi dan ta'adda ne kuma an san wurin da yake, don haka babu dalilin da zai sa a kama mahaifinsa.

Wata majiyar da jaridar ta ambato ta yi ikirarin cewa Turji ya aike da gargaɗi zuwa "ƙauyuka masu ƙawance" yana mai neman su fice.

Wani mazaunin garin Shinkafi, Mohammed Sani, ya yi zargin cewa wani makami mai linzami da aka harba cikin garin ya lalata sassan gidan sarki.

Sai dai kuma, rundunar yan sanda bata tabbatar da ci gaban ba.

A wani labari na daban, wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun sake kai hari Igangan, ƙaramar hukumar Ibarapa ta arewa, jihar Oyo, da daren ranar Jumu'a, inda duka kashe mutum huɗu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Sai dai jami'an tsaron sa kai na yankin sun samu nasarar fatattakar maharan kafin su yi mummunar ɓanna.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta gaza magance matsalar tsaro - Kukah ya fada wa Amurka

Kwamandan jami'an tsaron Amotekun a ƙaramar hukumar Ibarapa, wanda aka bayyana sunansa da Muri, ya na daga cikin waɗanda suka rasa ransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel