"Ka kiyaye ni," Gwamnan Zamfara ya gargadi mataimakinsa

"Ka kiyaye ni," Gwamnan Zamfara ya gargadi mataimakinsa

  • Gwamna Matawalle ya gargadi mataimakinsa da ya san cewa ruwa ba sa’an kwando ba ne
  • Gwamnan ya ce ba zai jure wa rashin ladabi daga mataimakin nasa ba sam-sam
  • A cewarsa ya fi karfin ya shiga sa-in-sa da mataimakin nasa

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Asabar ya ce ba zai yarda da halin rashin ladabi daga mataimakinsa, Mahdi Aliyu ba, rahoton PremiumTimes.

Matawalle ya fusata ne kan wani taron siyasa da aka yi kwanan nan wanda mataimakin gwamnan ya yi domin sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar hamayya ta PDP.

Dukkansu sun shigo gwamnati ne a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar PDP amma Matawalle da kusan dukkanin zababbun shugabanni a jihar a watan da ya gabata, sun sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC.

Mun kawo muku a baya cewa majalisar dokokin jihar ta fara shirin ladabtar da Mataimakin Gwamnan saboda gudanar da taron yayin da kashe-kashen ‘yan bindiga ke ci gaba da ta’azzara a Zamfara.

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC

Wannan ya haifar da ce-ce-ku-ce kan cewa ‘yan majalisar na son yin amfani da batun wajen tsige Mista Aliyu, wanda ya ki bin su zuwa APC.

"Ka kiyaye ni," Gwamnan Zamfara ya gargadi mataimakinsa
"Ka kiyaye ni," Gwamnan Zamfara ya gargadi mataimakinsa Hoto: Zamfara Governor
Asali: Twitter

Majalisar ta gayyaci Mista Aliyu ya bayyana a gabanta domin yin bayanin dalilin da ya sa ya gudanar da taron ba tare da la’akari da yanayin tsaro ba sannan “ga rashin mutunta shawarwari daga hukumomin tsaro a jihar.”

Gwamna Matawalle ya tsawata kan mataimakin nasa a yayin da yake hira da Sashin Hausa na DW a ranar Asabar.

Yace:

“A matsayina na gwamnan jihar, na yi alkawarin aiki tare da mataimakin gwamnan ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba. Amma ba zan jure wa halin rashin girmamawa daga gare shi ba.
"Ba zan shiga sa-in-sa tare da shi ba amma idan ya kushe ni, zai ji ni sarai," in ji gwamnan.
“Dukkanmu mun amince da dakatar da duk wani taron siyasa na maraba da ‘yan siyasa cikin jihar tunda mun rasa wadansu daga cikin magoya bayanmu yayin da suke maraba da mu.

Kara karanta wannan

Ta’addanci: Mataimakin gwamnan Zamfara ya shiga gagarumin matsala bayan gangamin PDP

“Kamata ya yi mataimakin gwamnan ya sanar da ni duk abin da ya shirya yi. Kasancewarmu a jam’iyyun siyasa daban ba yana nufin ni yanzu ba shugabansa ba ne. Tun ficewata daga PDPn, ya daina tarayya da ni.

Mataimakin gwamnan bai maida martani ga kalaman gwamnan ba.

Lambobin wayarsa da aka sani ba sa shiga da safiyar Asabar din nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel