2023: Cancanta za mu duba wajen zabar Shugaban kasa, kungiya ta bayyana zabinta

2023: Cancanta za mu duba wajen zabar Shugaban kasa, kungiya ta bayyana zabinta

  • Kungiyar National First Movement, ta nuna goyon bayanta ga kudirin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na neman kujerar shugaban kasa a 2023
  • A cewar kungiyar tsarin mulkin karba-karba baya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka cancanta za ta bi a wajen zabar magajin Shugaba Buhari
  • Kungiyar ta kuma ja hankalin masu ruwa da tsaki a kasar da su fifita cancanta da kwarewa yayin da zabukan 2023 ke gabatowa don magance dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta

Wata kungiya mai suna National First Movement, ta nuna goyon bayanta ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya ce mulkin karba-karba ya saba wa kundin tsarin mulki.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa cancanta da karfin isar da aiki su ya kamata su mamaye sararin siyasarmu yayin da 2023 ke gabatowa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum

Kara karanta wannan

2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu

2023: Cancanta za mu duba wajen zabar Shugaban kasa, kungiya ta bayyana zabinta
Kungiyar ta nuna goyon bayanta ga takarar Gwamna Yahaya Bello a matsayin shugaban kasa a 2023 Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Ta gargadi masu ruwa da tsaki a kasar da su fifita cancanta da kwarewa yayin da zabukan 2023 ke gabatowa don magance dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta.

Ta nuna rashin amincewa da kiran da Ohaneze Ndigbo ta yi kwanan nan cewa a mika mukamin Shugaban kasa zuwa yakin Kudu maso Gabas, tana mai bayyana kiran a matsayin abin da ya saba wa kundin tsarin mulki.

A wata sanarwa a ranar Laraba ta jagoranta, Chris Nwaokobia Jnr, kungiyar ta yi ikirarin cewa taron 1998 a Hukumar Jami’o’i ta Kasa, Abuja wanda Ohanaeze Nd’Igbo ya ambata bai sasanta batun shugabancin karba-karba ba.

“Ee, akwai maganganu masu gamsarwa game da bukatar mulkin karba-karba amma ba a yi yarjejeniya ka wannan ba. Yana nan a rubuce cewa 'yan watanni bayan nan, Cif Alex Ekwueme, Cif Jim Nwobodo da wasu kalilan a wajen yankin Kudu maso Yamma za su fafata don neman tikitin Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP da Cif Olusegun Obasanjo wanda shi ne babban dan takarar na Kudu maso yamma a zaben fidda gwani na PDP. Don haka a ina ne kuma yaushe aka tsara shugabancin karba-karba ?,” kungiyar ta tambaya.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

“Ni dan Najeriya ne daga kabilar Ibo, kuma ban yarda da shugabancin karba-karba ba kuma akwai miliyoyin ‘yan Ibo da suka yi imanin cewa cancanta da iyawa dole ne ya kamata su mamaye sararin siyasar mu yayin da 2023 ke gabatowa.
“Zan iya bayyana cewa abin da wadanda suka yi imani da Shugabancin Ibo za su yi shi ne sanya dabaru da diflomasiyya maimakon yin bita da kulli, saboda wadanda suka yi imani da cancanta da iya aiki a matsayin abunda ake bukata daga shugaba a 2023 ba za su zama matsorata ba.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Dalilin da yasa Gwamnan Zamfara ba zai sauka daga kujerarsa ba, Jigon APC

"Ina rokon fitaccen shugaban Ohaneze Nd'Igbo Cif George Obizor da ya jagoranci kakakin kakakin kungiyar domin Ndigbo kwararrun daliban tarihi ne kuma ba sa sanya karya da yaudara wajen cimma manufarsu ta kowani hali."

2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

A gefe guda, mun ji cewa ‘yan majalisar dokokin jihohin Arewa sun ce arewa ta cancanci ci gaba da rike shugabancin kasar bayan ficewar Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

‘Yan majalisar sun yi jayayya a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, cewa yankin kudu ya yi mulki na shekaru 14 yayin da arewa za ta yi mulki na shekaru 10 a karshen mulkin Shugaba Buhari, jaridar Leadership ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa sun taru ne a Abuja a kan kudirin neman takarar gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel