Labari Da Ɗuminsa: Annobar Korona Ta Hallaka Magajin Garin Johannesburg

Labari Da Ɗuminsa: Annobar Korona Ta Hallaka Magajin Garin Johannesburg

  • Mr Geoff Makhubo,magajin garin birnin Johannesburg a kasar Afirka ta Kudu ya rasu
  • Makhubo ya rasu ne sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 da ya kamu tun watan Yuni
  • Eunice Mgcina, mukadashin magajin garin Johannesburg, ta tabbatar da rasuwar Makhubo

Geoff Makhubo, magajin garin birnin Johannesburg a kasar Afirka ta Kudu ya mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 da aka fi sani da korona, The Cable ta ruwaito.

Mlimandlela Ndamase, mai magana da yawun birnin, ya ce an kwantar da Makhubo ne a asibiti bayan an gano yana dauke da kwayar cutar a watan Yuni.

DUBA WANNAN: Kano: Ɗalibi ya cinnawa kansa wuta saboda bai samu kuɗin biyan jarrabawar NECO ba

Labari Da Ɗuminsa: Annobar Korona Ta Hallaka Magajin Garin Johannesburg
Labari Da Ɗuminsa: Annobar Korona Ta Hallaka Magajin Garin Johannesburg
Asali: Original

Ya ce daga baya cutar ta yi ajalin magajin garin.

Makhubo yana da shekaru 53 a duniya.

Mukadashin magajin garin Johannesburg ta tabbatar da rasuwar Makhubo

A cewar jaridar kasar Afirka ta Kudu ta Sunday Times, Eunice Mgcina, mukadashin magajin gari kuma mamba a kwamitin lafiya da cigaba, MMC, ta bukaci masu zaman makoki kadu su tare a gidan mamacin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun dira garuruwa a Zamfara, sun hallaka mutum 42

Kasar Afirka ta Kudu na fama da annobar korona zagaye na uku da mugunyar nau'in kwayar cutar korona mai kisa da bazuwa da wuri ta Delta.

KU KARANTA: An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

Mgcina ta ce:

"Mun yi fatan magajin garin zai ci galaba kan cutar ya kuma dawo aiki ya jagoranci birnin a yayin da muke fuskantar annobar da ta janyo matsaloli ga rayuwan mutane da sana'o'insu. Amma, hakan bai yiwu ba."
"Muna mika sakon ta'aziyyar mu ga matarsa, yaransa mata da mahaifiyarsa da sauran yan uwansa, abokai da abokan aiki."

Marigayi Makhubo ya zama magajin gari ne a watan Yunin 2019.

Bayan 11 sun mutum da farko, mutum 4 ƴan gida ɗaya sun sake mutuwa bayan cin abinci mai guba a Kwara

A wani labarin, wasu mutane hudu yan gida daya sun mutu sakamakon guda da suka ci a abinci, wata daya bayan wasu mutum 11 yan gidan sun mutu bayan shan maganin gargajiya, hukumar tsaro ta NSCDC ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Bidiyon Shagari yana kunna sigari lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama'a

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin na baya-bayan ya faru ne a safiyar ranar Alhamis a kauyen Olori a Banni, karamar hukumar Kwara ta Arewa a jihar Kwara.

Kakakin ya ce babban jami'in hukumar na yankin, Taofeek ya shawarci sauran yan gidan da suka ci abinci iri daya da wadanda suka rasu su tafi asibiti a yi musu gwaji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel