An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

  • Yan sanda sun kama wasu mutum uku da ake zargi da mallakar kudin jabu fiye da Naira miliyan 15
  • Mutanen dai sune Fasto Sabastine, Emmanuel Aka Zuwa da wani Umar Mohammed da aka kama a Otel
  • Wadanda ake zargin sun amsa laifin mallakar kudin jabun suna mai cewa wani Nifom ne ya sayar musu da kudin jabun a Makurdi

Ƴan sanda a jihar Niger sun yi holen wasu mutane uku da ake zargi da mallakar kudaden jabu ƴan dubu-dubu da adadinsu ya kai Naira miliyan 15.8, Guardian NG ta ruwaito.

Wadanda ake zargin sune Fasto Sabastine Dabu, ɗan shekara 48 daga Zuru, jihar Kebbi, Emmanuel Aka Zuwa, ɗan shekara 42 daga ƙauyen Adi, ƙaramar hukumar Buruku, jihar Benue da Umar Mohammed, ɗan shekara 50 daga Pandagori, ƙaramar hukumar Rafi, jihar Niger.

Mutane uku da aka kama da kudin jabu a Niger
Mutane uku da aka kama da kudin jabu a Niger. Hoto: Guardian NG
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Abin da Yan Sanda suka ce yayin holen wadanda ake zargi

Guardian ta ruwaito cewa yayin holen wadanda ake zargin a hedkwatar yan sanda a Minna, kakakin yan sanda Wasiu Abiodun ya yi bayanin cewa ƴan sandan ƙaramar hukumar Kontagora, jihar Niger ne suka kama su.

Ya ce:

"Emmanuel, wanda shine jagaba wurin kitsa laifin an kama shi da N15.830 million wato Naira miliyan sha biyar da dubu ɗari takwas da talatin, a Otel a Kontagora, tare da Fasto Sabastine da Umar Mohammed da ake zargin wakilin Emmanuel ne."

Kakakin yan sandan ya ce Emmanuel ya amsa cewa ya aikata laifin, yana mai ikirarin cewa ya siya kudin bogin a kan N15,000 daga wani Nifom a Katsina Ala jihar Benue. (Wanda yanzu ake nema).

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: An yi wa shugaban kasar Haiti kisar gilla a gidansa

Abiodun ya kuma ce ya hadu da Fasto Sabastine ne a taron coci a Makurdi, Benue inda ya masa alƙawarin zai taimaka masa siyar da kuɗin bogin.

Yayin da shi kuma Umar Mohammed, Fasto Sabastine ne ya ɗauki shi kwangila domin ya sadu da mai siya a Otel din.

Ana cigaba da bincike kuma za a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala.

Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel