Da duminsa: Yan bindiga sun dira garuruwa a Zamfara, sun hallaka mutum 42
- Kuma dai, yan bindiga sun sake hallaka mutane a Zamfara
- Wannan ya biyo bayan sauya shekar gwamnan zuwa APC
- Gwamna Matawalle yace ya koma APC ne don samar da zaman lafiya a jihar
Akalla mutum arba'in da biyu tsagerun yan bindiga suka hallaka yayinda suka kai hari kauyuka biyar a karamar hukumar Maradun, a jihar Zamfara da daren Alhamis.
Garuruwan da aka kai hari sun hada da Tsauni, Gudan-Baushi, Gidan-Adamu, Wari da Gudan-Maidawa, cewar rahoton Punch.
Wani dan garin, Malam Buba Faru, ya ce yan bindiga sun dira garin kan babura sama da 100.
Buba yace dirarsu ke da wuya, suka fara harbin mutane suna kona gidaje da runbunan abinci.
Yace:
"Suna harbin kan mai uwa da wabi yayinda suka shiga garuruwan. Sun kai wa manoman dake gonakinsu hari.
"Zuwa yanzu dai jami'an tsaro da yan sa kai sun gano gawawwaki 42
Buba ya kara da cewa za'a yi jana'izar mamatan ranar Juma'a.
KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido
DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo
Mutum 35 kadai aka kashe
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya ce mutum 35 kadai aka kashe a tattaunawarsa da jaridar Punch.
A cewarsa, an tafi da gawawwakinsu garun Faru inda za'a biznesu.
Kaakin yan sandan yace:
"Jami'an hukumar basu samu damar shiga garuruwan lokacin da ake kai harin ba saboda rashin kyan hanya."
Ya kara da cewa yan sanda na kokari matuka don damke yan bindigan.
A bangare guda, wasu ‘yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun sace shugaban kwalejin kimiyyar dabbobin Bakura, Habibu Mainasara, da ke jihar Zamafara a safiyar ranar Lahadi, Channels Tv ta ruwaito.
Wata majiya ta ce, 'yan bindigan sun dauke shi ne da misalin karfe 2:00 na daren yau a gidansa da ke karamar makarantar sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Bakura.
Asali: Legit.ng