Labari Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Harbe Shugaban SEDI Har Lahira

Labari Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Harbe Shugaban SEDI Har Lahira

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun halaka shugaban SEDI Farfesa Samuel Ndubisi a Enugu
  • Rundunar yan sandan jihar Enugu ta bakin kakakinta Daniel Ndukwe ta tabbatar da afkuwar lamarin
  • Yan bindigan sun kuma halaka dan sandan da ke tsaron Farfesa Ndubisi suka kuma raunata direbansa

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Laraba, sun bindige Samuel Ndubisi, shugaban cibiyar habbaka kayayyakin kimiyya, SEDI, a jihar Enugu, Kudu maso gabashin Nigeria, Premium Times ta ruwaito.

Kamfanin dillancin labarai ta NAN ta ce an kashe Farfesa Ndubisi tare da dan sanda mai tsaronsa a Centenary City Junction a babban titin Enugu zuwa Port Harcourt, rahoton The Punch.

KU KARANTA: Bethel Baptist: Ƴan bindiga sun nemi a basu shinkafa da wake da zasu ciyar da ɗalibai 121 da suka sace a Kaduna

Labari Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Harbe Shugaban SEDI Har Lahira
Labari Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Harbe Shugaban SEDI Har Lahira. Ndubisi Samuel (Prof)
Asali: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa direban motan da suke ciki shima ya samu raunin bindiga kuma an garzaya da shi wani asibiti da ba a bayyana sunan ba domin yi masa magani.

Rundunar Yan Sanda ta tabbatar da mutuwar Ndubisi

Mai magana da yawun yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Mr Ndukwe, mai mukamin sufritandan yan sanda, ya ce a yanzu ba a kammala tattare bayani game da afkuwar lamarin ba a lokacin hada wannan rahoton.

KU KARANTA: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Lamarin ya faru ne misalin karfe 4 na yamma a cewar mai magana da yawun yan sandan.

Ya ce:

"Bayani game da harbin da aka yi a yau 07/07/2021 misalin karfe 4 na yamma a kan babban titin Enugu-PortHarcourt, ya yi sanadin mutuwar wani mutum da dan sanda mai tsaronsa duk da cewa ba a samu cikaken bayani ba.
"Sai dai, an fara gudanar da bincike. Za mu bada karin bayani nan gaba."

'Yan bindiga sun kashe mutum 19 a Katsina, sun ƙona gidaje sun sace dabbobi masu yawa

A wani rahoton, a kalla mutane 19 ne suka mutu sannan wasu dama an neme su an rasa bayan yan bindiga kan babura sun kai hari kauyen Tsauwa a karo na biyu a karamar hukumar Batsari na jihar Katsina a yammacin ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani majiya daga kauyen ya ce maharan sun afka garin ne misalin karfe 5.45 na yamma.

Yan bindigan sun tarwatsa mazauna kauyen suka rika binsu a kan babura, suka harbe 19 har lahira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel