Bethel Baptist:Ƴan bindiga sun nemi a basu shinkafa da wake da zasu ciyar da ɗalibai 121 da suka sace a Kaduna

Bethel Baptist:Ƴan bindiga sun nemi a basu shinkafa da wake da zasu ciyar da ɗalibai 121 da suka sace a Kaduna

  • Yan bindigan da suka sace dalibai daga makarantar Bethel Baptist da ke Kaduna sun nemi a basu kayan abinci su ciyar da daliban
  • Yan bindigan sun gabatar da wannan bukatar ne a yayin da suka kira mahukunta makarantar a wayan tarho ranar Talata
  • Yayin wayan da suka yi da jami'an makarantar, sun kuma umurci wani dalibi ya kidaya sauran yan uwansa da ya tabbatar su 121 ke hannun yan bindigan

Yan bindiga, wadanda suka kai hari Maraban Rido a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna a ranar Litinin suka sace wasu dalibai daga Bethel Baptist High School, Damishi, sun tuntubi masu makarantar suna neman kayan abinci, The Punch ta ruwaito.

Rahoton na The Punch ya ce yan bindigan sun nemi a basu kayan abinci irinsu Shinkafa, wake, kayan kanshi da mai domin su ciyar da daliban.

Makarantar Bethel Baptist High School a Kaduna
Makarantar Bethel Baptist High School a Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Wani ma'aikacin makarantar da ya nemi a boye sunansa, ya ce yan bindigan sun tabbatar da cewa dalibai 121 ne ke hanunsu.

A cewar wani babban jami'in makarantar, yan bindigan sun kira su a ranar Litinin sun kyale daya daga cikin daliban ya yi magana da wani ma'aikacin makarantar.

An gano cewa sun sake kira a ranar Talata sun kyalle daliban manyan aji na biyu, mace da namiji sunyi magana da wani babban jami'in makarantar.

Daliban manyan ajin sun tabbatar da cewa su 121 ne ke hannun masu garkuwar da mutane.

KU KARANTA: Bidiyon Dala: Kotu Ta Umurci Ganduje Ya Biya Ja’afar Ja’afar Tara Bayan Janye Ƙara

Jami'in makarantar wanda ya yi magana da The Punch, ya ce:

"A lokacin da kiran ta shigo, yan bindigan sun fara magana da babban jami'in makarantar. Sun ce dalibin babban aji ya kirga daliban kuma yaron ya tabbatar dalibai 121 ne ke tsare. Sun kuma nemi abinci kamar shinkafa da wake da mai domin su ciyar da daliban."
"Daga bisani, dalibin babban ajin, wanda ya kirga daliban ya ce su 121 ke hannun yan bindigan."

El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna

A wani rahoton, Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin rufe wasu makarantu 13 nan take a wurare daban-daban a jihar, The Cable ta ruwaito.

Shugaban sashin kula da ingancin kayayyaki na ma'aikatar ilimi na jihar Kaduna, Umma Ahmed ce ta fitar da sanarwa.

An aike da sanarwar da shugabannin makarantu masu zaman kansu da abin ya shafa, sakon na mai cewa nan take za su rufe makarantun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164