Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

  • Dakarun sojojin Nigeria na Operation Hadin Kai, OPHK, a Borno sun yi nasarar kama yan Boko Haram biyu
  • Direktan sashin watsa labarai na rundunar sojoji, Onyema Nwachukwu ya ce a ranar 3 ga watan Yuli aka kama su a kauyen Labe
  • Nwachukwu ya ce an kama su dauke da kayayyaki da yawa da suka hada da maganin karfin maza, gurneti na hannu, mota, kekuna, diga dss

Dakarun sojojin Nigeria na Sector 1 Operation Hadin Kai (OPHK) tare da taimakon Yan Sa-Kai na Civilian JTF, a ranar 3 ga watan Yuli sun kama wasu yan ta'addan kungiyar Boko Haram biyu, Premium Times ta ruwaito.

LIB ta ruwaito cewa direktan sashin watsa labarai na rundunar sojoji, Onyema Nwachukwu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce sojojin sun kama wasu kayayyaki da aka siyo domin kaiwa yan ta'addan.

Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno
Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Abubuwan da aka samu a hannun yan ta'addan

Mr Nwachukwu ya ce sun kama gurneti na hannu, diga daya, mota daya, kekuna biyar, wayoyin salula biyu (Tecno da Infinix), man fetur da man juye.

Ya kuma kara da cewa sojojin sun kwato kwayoyi masu bugarwa da magungunan kara karfin maza, magungunan kwari da sauro, kayan abinci da wasu abubuwan.

Hotunan Ƴan Boko Haram Da Sojoji Suka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno
Hotunan Ƴan Boko Haram Da Sojoji Suka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno. Hoto: LIB
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kungiyoyin CAN da HURIWA sun buƙaci El-Rufai ya yi murabus bayan garkuwa da ɗalibai 26 a Kaduna

A cewarsa, rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba yayin aikinta na bincika yankin domin tarwatsa sansani da mabuyar yan ta'addan da suka yi saura.

Ya ce, "Yayin sintiri, dakarun sojoji sun yi karo da wasu yan ta'adda a kauyen Labe wadanda suka yi yunkurin tserewa amma nan take aka cafke su cikin gaggawa.
"Babban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Faruk Yahaya, ya jinjinawa kuzarin sojojin, yana mai cewa su cigaba da ragargazar yan ta'addan har sai sun tabbatar sun fatattake su sannan su mamaye yankin."

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

An fahimci cewa cewar yan sandan sirrin na Nigeria sun tabbatar da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho yayin da sauran aka ci galaba a kansu aka kama su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel