Annobar COVID-19: Babu Najeriya a cikin kasashen da bankin Duniya zai ba Naira Tiriliyan 2

Annobar COVID-19: Babu Najeriya a cikin kasashen da bankin Duniya zai ba Naira Tiriliyan 2

  • Bankin Duniya ya ki zabar Najeriya cikin kasashen da zai ba tallafin kudi
  • Kasashe 51 za su ci moriyar tallafin sayen magungunan cutar Coronavirus
  • Wadannan kasashe za su tashi da kusan Naira tiriliyan 2 a kudin Najeriya

Najeriya ba ta cikin jerin kasashe masu taso wa da bankin Duniya ya zaba, za a ba gudumuwar kudi da nufin su mallaki magungunan cutar COVID-19.

Kamar yadda The Nation ta fitar da rahoto dazu, kananan kasashe har 51 bankin ya ware domin a ba su fam dala biliyan hudu, su saye magungunan cutar.

A sabon rahoton da bankin Duniyar ya fitar na wadanda za a ba tallafin kudin sayen magunguna, ba a ga sunan Najeriya ba, duk da akwai makwabtanta.

KU KARANTA: Allurar rigakafin kwayar COVID-19 ta iso Najeriya

Jaridar ta ce fiye da rabin kasashen da aka zaba da nufin a ba wannan tallafi, sun fito ne daga Afrika.

Babu sunan Najeriya a kasashen da aka ambata a shafin yanar gizon bankin. Wannan mataki da babban bankin Duniyan ya dauka ya ba mutane mamaki.

Jerin kasashen da za a ba tallafin sayen magunguna

Kasashen da su ka yi dace sun hada da; Ghana, Guinea, Guinea Bissau, Benin, Cabo Verde, kasar Jamhuriyyar Kongo, Côte d’Ivoire, Habasha da Gambiya.

Sauran kasashen da su ke ciki sun hada da Madagascar, Malawi, Mozambique, Jamhuriyyar Nijar, Papua, New Guinea, Filifins, Ruwanda da kuma Sanagal.

Rigakafin COVID-19
Buhari ya na karbar allurar COVID-19 Hoto: youthpartyng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Jihohi 7 a Arewacin Najeriya za su amfana da tallafin COVID-19

Kamar yadda aka bayyana a shafin, akwai Sierra Leone, Kudancin Sudan, Siri Lanka, Sudan, Togo, Tunisiya, Ukraine, Yemen, da Zambiya a cikin jerin.

Kokarin da bankin Duniya yake yi na yakar Coronavirus

Darektan gudanarwa na bankin mai ba kasashen Duniya bashi, Axel van Trotsenburg, ya ce su na bada wannan kudi ne domin su mallaki magungunan cutar.

Axel van Trotsenburg ya ce su na kokarin kawo karshen kalubalen da ake samu wajen yakar cutar.

Kwanakin baya kun samu labari cewa Bankin Duniya zai taimaka wajen fitar da mutum miliyan 100 daga talauci a Najeriya kamar yadda gwamnati ta ke buri.

Shugaban bankin Duniya, David Malpass, ya bayyana wannan a taron IMF da aka shirya kwanaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel