Bankin Duniya zai taimaka wajen fitar da mutum miliyan 100 daga talauci a Najeriya
- Gwamnatin Najeriya ta ci burin ceto mutane miliyan 100 daga talauci
- Babban bankin Duniya ya yi alkawari taimakawa Gwamnatin Tarayya
- Shugaban bankin Duniya, David Malpass, ya bayyana wannan a taro
A ranar Laraba, 7 ga watan Afrilu, 2021, shugaban babban bankin Duniya, David Malpass, ya ce su na maida hankali game da talaucin da ke Najeriya.
Kamar yadda This Day ta fitar da rahoto, David Malpass ya yi alkawarin taimaka wa gwamnatin tarayya wajen kubutar da mutane miliyan 100 daga talauci.
Shugaban bankin Duniyan ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da 'yan jarida a taron kungiyar bada lamuni ta IMF da ake yi a birnin Washington.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace Basarake a Najeriya
Da yake jawabi a Amurka jiya, Mista David Malpass ya ce za su tallafa wa gwamnati wajen kokarin samar da ayyukan yi, jawo cigaban tattalin arziki da raba arziki.
A cewar David Malpass, bankin Duniya ya taimaka wa Najeriya ta harkar bashi, da tabbatar da cewa ana gudanar da sha’anin kudi ba tare da an yi rashin gaskiya ba.
Kwanakin baya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawari gwamnatinsa za ta tsamo mutane miliyan 100 daga masifar talauci a cikin shekaru goma masu zuwa.
Malpass ya ce bankin Duniya zai cigaba da sa ido a kan bashin da ke kan kasashen da karkashin ta.
KU KARANTA: Akwai yiwuwar Majalisar Najeriya ta kyale a sanya Hijabi a gidan soja
Da yake amsa wata tambaya a jiyan, Malpass ya ce bankin Duniya ya hada-kai da Najeriya domin sa-ido a kan yadda gwamnatin tarayyar kasar ta ke batar da kudin al’umma.
Babban bankin ya ce abin da za su maida hankali a kai shi ne jawo masu hannun jari su zuba kudinsu a kasashe domin samar da abubuwan more rayuwa da aikin yi.
A makon nan kun ji cewa arzikin da manyan gawurtattun masu kudin da ake ji da su a Najeriya su ka mallaka ya kara yawa a bana kamar yadda mujallar Forbes ta nuna.
Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya tashi da Naira Tiriliyan 1.3, yayin da shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdussamad Rabiu ya samu fiye da Naira Miliyan 800 a shekarar 2020.
Asali: Legit.ng