COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya za su mori tallafin $900,000

COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya za su mori tallafin $900,000

- Asusun tallafawa Noma na Kasa da Kasa ya bada tallafi ga manoma a yankin arewacin Najeriya

- Asusun ya zabi wasu jihohi da COVID-19 ya shafa a arewa ne domin tallafa musu da $900,000

- Kimanin mutane 8,000 za su ci gajiyar wannan tallafi a cikin jihohi bakwai a arewacin Najeriya

Asusun Tallafawa Noma na Kasa da Kasa, IFAD, ya ba da tallafi na farko na dala 900,000 don tallafawa mafi munin ƙananan 'yan kasuwa da gidajen karkara a Arewa da rikicin COVID-19 ya rutsa dasu.

A cewar kungiyar, tallafin wanda aka bayar ta hanyar Rukunan Talakawan Karkara (RPSF), an kuma bayar da shi ne ga magidanta da kananan manoma don sake ginawa da murmurewa a lokacin rikicin.

IFAD ta fadi haka ne a cikin wata sanarwa da Vera Onyeaka-Onyilo, mai ba da shawara kan kula da ilimi da sadarwa na shirin IFAD na Najeriya ta gabatar ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma'a.

KU KARANTA: COVID-19 ta shiga jerin kalubalen duniya kamar ta'addanci, rashawa, in ji Buhari

COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya sun mori tallafin $900,000
COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya sun mori tallafin $900,000 Hoto: VOA News
Asali: UGC

Sanarwar ta ci gaba da lura cewa Zainab Ahmed, Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren kasa da kuma Nadine Gbossa, Daraktan Yankin IFAD na Afirka ta Yamma da Tsakiya sun sanya hannu kan yarjejeniyar tallafin.

A cewar sanarwar, kudin zai taimakawa kananan manoma marasa karfi a jihohin Arewa bakwai da suka hada da Borno, Jigawa, Katsina, Kebbi, Sokoto, Yobe, da Zamfara

“Gwamnatin tarayyar Najeriya da Asusun Tallafawa Noma na Kasa da Kasa na Majalisar Dinkin Duniya (IFAD) suna aiki tare don rage tasirin cutar COVID-19 a kan kananan ayyukan manoma da samar da abinci a cikin gida a jihohin Arewa maso Gabashin kasar.

“A karkashin jagorancin Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara, sama da masu karamin karfi 8,000 a Arewacin Najeriya za su sami tallafin kayan gona da wani kunshi wadanda suka hada da tsaba mai karfin yanayi.

KU KARANTA: An sace tawagar abokan ango a jihar Taraba

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta fara raba wa matan karkara kudi Naira dubu 20 a karkashin shirin bayar da tallafi ga matan karkara 4,000 a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar gwamnatin tarayya, za a zabi matan 4,000 a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.

An gabatar da shirin a cikin shekarar 2020 don ci gaba da aiwatar da tsarin zamantakewa a Gwamnatin Shugaba Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel