Yanzun nan: Allurar rigakafin kwayar cutar COVID-19 ta iso Najeriya

Yanzun nan: Allurar rigakafin kwayar cutar COVID-19 ta iso Najeriya

- Da tsakar ranar yau ne allurar rigakafin Korona ta iso filin jirgin Nnamdi Azikwe, Abuja

- Allurar ta samu tarbar fitattun 'yan Najeriya, ciki har da ministan lafiya da na yada labarai

- Wannan shine kaso na farko na allurar, wanda ke dauke da kusan allurai miliyan 4 na COVID-19

Allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca da NAFDAC ta amince dasu sun iso kasar Najeriya da tsakar ranar Talata, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta wani kamfanin jirgin sama na Emirates, Channels Tv ta ruwaito.

Shugaban kwamitin tsaro na shugaban kasa (PTF) kan COVID-19, Boss Mustapha, ya fada a ranar Asabar cewa Najeriya za ta karbi kaso na farko na kimanin allurai miliyan 4 na COVID-19.

KU KARANTA: Dillalan shanu sun shiga hannun DSS saboda hana kai kaya Kudancin Najeriya

A filin da za a karbi kayan rigakafin akwai manyan jami'an gwamnati da suka hada da Shugaban PTF, Boss Mustapha; da Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed; da Darakta-Janar na Cibiyar hana yaduwar cututtuka (NCDC) Chikwe Ihekweazu.

KU KARANTA: Yajin aiki: Kayayyakin abinci sun yi tashin gwauron zabo a kudancin Najeriya

Yanzun nan: Allurar rigakafin kwayar cutar COVID-19 ta iso Najeriya
Yanzun nan: Allurar rigakafin kwayar cutar COVID-19 ta iso Najeriya Hoto: BBC
Asali: UGC

“An ce mana mu bude asusu da Afreximbank a karkashin Tarayyar Afirka; Mun riga mun yi hakan tuni saboda za mu biya kudin wani bangare na allurar rigakafin. \

Alurar rigakafin ta COVAX kyauta ce, ba za mu karbi ko kobo ba, an samar da ita ne ta hanyar gudunmawa,” in ji Mistan lafiya.

Yanzun nan: Allurar rigakafin kwayar cutar COVID-19 ta iso Najeriya
Yanzun nan: Allurar rigakafin kwayar cutar COVID-19 ta iso Najeriya Hoto: BBC
Asali: UGC

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari, Mataimakinsa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha da sauran fitattun ‘yan Najeriya za su kasance cikin sahun farko na 'yan Najeriya da zasu yi allurar rigakafin COVID-19 ta gidan talabijin kai tsaye.

Ana sa ran za su fara allurar ta farko a ranar Asabar, 6 ga Maris. Babban Darakta/Shugaba, na Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Dokta Faisal Shuaib, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a taron hadin gwiwa na kasa da aka yi na Kwamitin Shugaban Kasa (PTF) kan COVID-19.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel