Shugaba Buhari ya sa hannu a biya tsofaffin Ma’aikata kudin fansho da su ke bi bashi

Shugaba Buhari ya sa hannu a biya tsofaffin Ma’aikata kudin fansho da su ke bi bashi

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bukatar da PenCom ta kawo masa
  • Za a biya tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya hakkokin kudin da su ke bi
  • Hukumar PenCom ta ce karin albashi da aka yi zai yi tasiri a kudin da za a biya

Jaridar This Day ta kawo labari cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da rokon da hukumar fansho ta kasa watau PenCom ta gabatar a gabansa.

Hukumar PenCom ta bukaci a ba ta dama ta biya bashin kudin da tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya su ke bi bashi a karkashin tsarin fanshon CPS na kasa.

A wani jawabi da PenCom ta fitar a ranar Laraba, ta ce an ware kudin da za a biya mutane hakkinsu.

KU KARANTA: Mu ne matsalar kasar nan ba komai ba - Buhari

Hukumar ta ke cewa za ta biya wadanda su ka yi ritaya daga gwamnatin tarayya ba tare da sun karbi fansho da kudin sallama ba, da kudin wadanda su ka rasu.

Sabon tsarin mafi karancin albashi zai shafi fansho

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma amince da biyan karin kudin da aka yi a kan tsarin mafi karancin albashi, wanda wannan canji ya sa fanshonsu ya karu.

A shekarar da ta wuce ne gwamnatin tarayya ta kawo sabon tsarin albashi inda kowane ma’aikaci ya koma tashi da akalla N30, 000, a maimakon N18, 000.

Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto, za a fara biyan wadanda su ka yi ritaya daga aiki daga Yulin 2014 da 10% na abin da suka tara a asusun fanshonsu.

Shugaba Buhari ya sa hannu a biya tsofaffin Ma’aikata kudin fansho da su ke bi bashi
Shugabannin hukumar PenCom ta kasa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Har gobe ana zalunci a PDP inji Buba Galadima

“An ware kudin da za a fitar domin a biya mutanen nan hakkokinsu. An zuba kudi a asusun ajiyar fansho na RSA na tsofaffin ma’aikatan da za a biya fanshonsu.”
"Ba da dadewa ba za a sanar da wadannan tsofaffin ma’aikata wadanda kudinsu yake hannunsu."

Jaridar ta ce hakan na zuwa ne bayan hukumar fanshon PTAD ta karbo fam Euro miliyan £26.5 daga Birtaniya, Wannan kudi sun kai Naira biliyan 13 a kudin gida.

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya koka da cewa Hukumar JAMB ta na kawo wasu sharudan shirme da ke sa mutane a wahala, ya ba gwamnatin tarayya shawara.

Shehin ya ce a maimakon a rika dankara kudi a TSA, a rage farashin sayen jarrabawar JAMB.

Asali: Legit.ng

Online view pixel