Sai wanda bai san ciwon kansa ba zai zauna a jam’iyyar PDP inji Injiniya Buba Galadima

Sai wanda bai san ciwon kansa ba zai zauna a jam’iyyar PDP inji Injiniya Buba Galadima

  • Injiniya Buba Galadima ya fito ya soki babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP
  • Fitaccen ‘Dan adawan ya zargi Jam’iyyar PDP da zalunci da rashin adalci
  • Galadima ya ke cewa PDP ba ta iya adawa ba, kuma ba za ta taba iyawa ba

Babban ‘dan adawan kasar nan, Injiniya Buba Galadima, ya yi tir da jam’iyyar PDP da ake tunanin ya na tare da ita, ya sake nesanta kansa daga jam’iyyar.

A wata hira da aka yi da Buba Galadima a gidan rediyon DW Hausa, ya bayyana cewa PDP ba iya aikin ta na adawa ba, ya ce jam’iyyar ba za ta taba iya wa ba.

Tsohon sakataren na jam’iyyar CPC (wanda ta narke a APC), ya ce ana zalunci a PDP ta yadda babu mai iya rike mukami sai wanda ke tare da wasu tsiraru.

KU KARANTA: Injiniya Buba Galadima ya roki Buhari ya nada shi Shugaban INEC

Akwai ‘Yan mowa da ‘Yan bowa a gidan PDP

DW Hausa ta wallafa bangaren wannan hira da ta yi da ‘dan adawar a shafin ta na Facebook, wanda ya tabbatar da cewa Galadima ba ya tare da jam’iyyar.

“Jam’iyyar PDP idan ka ce ta gaza ma ba ka yi laifi ba, domin ba ta iya adawa ba, ba ta taba adawa ba, ba za ta iya yin adawa ba.”
“Dadin dada wa, rashin adalcin nan da aka san ta da shi tun tuni, ya na nan, ya yi katutu a gindinta.”
“An yi wata da’ira a cikin tafiyar PDP, sai ‘Dan mora ne zai iya rike wata kujera, ko zai iya samun wani mukami.”
“To dukkan wani mutum da ya san ciwon kansa, ba zai zauna a wannan jam’iyya ba.”

KU KARANTA: Kowa zai gujewa Buhari kafin 2019 - Buba Galadima

Buba Galadima
Injiniya Buba Galadima Hoto: www.theinterview.ng
Asali: UGC

Masu karatu sun tofa albarkacin bakinsu

Mutane sun tofa albarkacin bakinsu bayan jin abin da Galadima yake fada. Ga kadan daga cikin martanin da ake yi masa a Facebook:

Muhammad Ibrahim Abdallah Shamsu ya rubuta:

“Allah ya kyauta, an ba ka kudi kenan!”

Shi kuma Aliyu Ibrahim Muhammad cewa ya yi:

“Dama ba ‘dan PDP ba ne, komai ya fada daidai ne.”

Muhammad Sabo-Sabo yake yi wa jam’iyyar mugun fata;

“Buba ya ji wuta, wallahi duk sun rude a PDP. Matsiyaciyar jam’iyya, in sha Allahu sai PDP ta tarwatse gaba-daya.”

Kwanakin baya, aka ji Buba Galadima ya na cewa shi ba ‘Dan PDP ba ne. Duk da ya taimaki Atiku Abubakar a zaben 2019, 'dan siyasar ya nesanta kansa da jam'iyyar.

'Dan siyasar ya bayyana wannan a taron da Premium Times Centre for Investigative Journalism ta shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel