Sheikh Ahmad Gumi ya koka da tsare-tsaren JAMB, ya ba Hukumar muhimman shawarwari

Sheikh Ahmad Gumi ya koka da tsare-tsaren JAMB, ya ba Hukumar muhimman shawarwari

  • Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ba hukumar JAMB wasu shawarwari
  • Shehin malamin ya ce an shigo da wasu ka’idoji na babu gaira babu dalili
  • Dr. Ahmad Gumi ya kawo shawarar a rage kudin da ake biya wajen rajista

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya tofa albarkacin bakinsa game da kiraye-kirayen da ake ta yi wa hukumar JAMB.

Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, a shafinsa na Facebook, ya bayyana yadda hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta ke kawo cikas.

Shahararren malamin ya ce JAMB ta yi kokari da ta kawo tsarin CBT ta yadda za a kawo sauki, sannan a rage satar amsa a jarrabawa, amma ya ce akwai aiki a gaba.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta san inda ‘Yan bindiga su ke - Gumi

“A 2019, mun kafa cibiyar CBT (wajen rubuta jarrabawa da na’urori) a makarantar nan ta Sheikh Abubakar Gumi da ke Tudun Wada, Kaduna. A shekarar, mutane 3000 su ka yi jarrabawar su hankali kwance.”

Masanin addinin ya koka da cewa zuwa 2020, lamarin ya canza, aka kawo wa masu shirya jarrabawa da dalibai tsare-tsaren banza da wofi, da ka’idojin shirme.

“Abin da ya faru shi ne wani ma’aikacinmu mai kokari da gaskiya, ya yi kuskuren jefar da layin lambar wayar sabuwar cibiyar, sai aka ki ba mu damar yin jarrabawa.”

Sheikh Ahmad Gumi ya ce an kai maganar batar layin (SIM) wajen ‘yan sanda, amma duk da haka sabon shugaban hukumar ta JAMB ya hana cibiyar amfani a 2020.

KU KARANTA: Za mu ware £2.6m domin kawo karshen Boko Haram – Ingila

Sheikh Ahmad Gumi ya koka da tsare-tsaren JAMB, ya ba Hukumar muhimman shawarwari
Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi Hoto: @AhmadAbubakarMahmudGumi
Asali: Facebook

“Wannan shekarar (2021), an sake maimaita abin da ya faru. Na yi mamaki da aka tura ‘diya ta zuwa Kujama ta yi jarrabawa, duk da halin rashin tsaro da ake ciki.”

Dr. Ahmad Gumi ya ce matsi da takura da hukumar ta ke yi ba abin kirki ba ne, sai ma nuna rashin sanin aiki.

Ya ce “Ina dalilin yin rajistar lambar NIN kafin a iya rubuta jarrabawa?

Haka zalika malamin ya yi kira ga gwamnati ta rage farashin jarrabawar UTME domin a taimaka wa ‘ya ‘yan marasa karfi maimakon JAMB ta rika maida wa gwamnati kudi.

Kwanan nan ne aka ji cewa hukumar tsaron farar kaya ta DSS ta gayyaci Sheikh Ahmad Gumi zuwa ofishinta, amma dai malamin musuluncin ya karyata wannan labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel