Ba addini ko kabilanci bane matsalar Najeriya, mune matsalar kanmu - Shugaba Buhari

Ba addini ko kabilanci bane matsalar Najeriya, mune matsalar kanmu - Shugaba Buhari

  • Buhari ya ce yan Najeriya ne matsalolin kansu ba harshe ko addini ba
  • Shugaban kasan ya bayyana yadda Igbo suka taimakesa amma Fulani suka juya masa baya
  • Ya karbi bakuncin magoya bayansa ranar Laraba

Shugaba Muhammadu Buhari ya tofa albarkacin bakinsa kan halin da Najeriya ke ciki, inda ya yanke cewa ba addini ko kabilanci bane matsalarmu, innama mune matsalar kanmu.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayansa na (MBO) Dynamic Support Group, yayinda suka kai masa ziyara fadar Aso Villa.

Mai magana da yawun shugaban kasan, Femi Adesina, a jawabin da ya saki ranar Laraba yace ya kungiyar sun kai wa Buhari gundarin ayyukan da ya gudanar cikin shekaru biyar a mulkinsa.

Buhari ya basu labarin irin gwagwarmayan da yayi a kotu tun lokacin da ya kara takara a 2003 har 2011 amma yan uwansu Alkalai Fulani suka juya masa baya yayinda wasu kabilun suka tsaya masa.

A cewarsa:

Na baku wannan labarin ne domin tabbatar muku matsalarmu ba kabilanci bane ko addini. Mune matsalar kanmu."

Shugaba Buhari yayi jawabi
Ba addini ko kabilanci bane matsala, mune matsalar kanmu - Shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng