Shugaba Buhari ya yi muhimman naɗi biyu a hukumar PPPRA

Shugaba Buhari ya yi muhimman naɗi biyu a hukumar PPPRA

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mr Atuonwo Obinna a matsayin shugaban PPPRA
  • Shugaban kasar ya kuma amince da sabunta nadin Mr Abdulkadir Saidu a matsayin babban sakatare a hukumar ta PPPRA
  • Mr Femi Adesina, mashawarcin shugaban kasa na musamman a bangaren watsa labarai ne ya fitar da sanarwar a ranar Juma'a

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin shugaba da kuma babban sakatare a hukumar daidaita farashin man fetur, PPPRA, Vanguard ta ruwaito.

An nada Mr Atuonwo Obinna a matsayin shugaba yayin da Mr Abdulkadir Saidu shi kuma aka sabunta nadinsa a matsayin babban sakatare na tsawon shekaru hudu, The Punch ta ruwaito.

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

Wannan na cikin wata sanarwa ne mai dauke da sa hannun mashawarcin shugaban kasa na musamman a bangaren watsa labarai, Mr Femi Adesina da ya fitar a ranar Juma'a a Abuja.

A cewar sanarwar, an nada Mr Atuonwo Obinna ne a matsayin shugaban kwamitin hukumar na tsawon shekaru hudu kamar yadda sashi na 2 (1-3) da 3 (a) na dokar hukumar PPPRA ta 2003.

KU KARANTA: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Zai maye gurbin Mohammed Buba wanda aka nada shugaban PPPRA a 2016 bayan hukumar kwadago na kasa, NLC, ta bukaci gwamnatin tarayya ta sauya mambobin kwamitin amintattu na hukumar.

A baya bayan nan, Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya.

A ranar 18 ga watan Yuni, ya amince da nadin sabbin sakatarin dindindin a hukumomin gwamnatin tarayya.

Ya kuma nada Balarabe Ilelah a matsayin shugaban hukumar kula da kafafen watsa labarai, NBC.

Gwamna Nasir El-Rufai ya naɗa sabon Sarki a Masarautar Lere

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya nada Injiniya Suleiman Umaru Lere a matsayin sabon sarkin masarautar Lere a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya kuma nada Rabarand Habila Sa'idu a matsayin sarkin Godogodo.

Sanawar da mashawarcin gwamnan na musamman kan kafafen watsa labarai, Mr Muyiwa Adekeye ya fitar a ranar Juma'a ta ce gwamnan ya amince da nadin ne bayan samun shawarwari daga masu zaben sarakuna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel