Da Ɗuminsa: El-Rufai ya naɗa sabon Sarki a Masarautar Lere

Da Ɗuminsa: El-Rufai ya naɗa sabon Sarki a Masarautar Lere

  • Gwamna Nasir El-Rufai ya nada Injiniya Suleiman Umaru Lere a matsayin sabon sarkin Lere
  • Gwamnan ya kuma amince da nadin Rabarand Habila Sa'idu a matsayin sarkin Godogodo
  • Gwamnan ya taya sarakunan biyu murna nadinsu ya kuma bukaci su yi amfani da matsayinsu wurin kawo zaman lafiya da cigaba

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya nada Injiniya Suleiman Umaru Lere a matsayin sabon sarkin masarautar Lere a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya kuma nada Rabarand Habila Sa'idu a matsayin sarkin Godogodo.

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Sanawar da mashawarcin gwamnan na musamman kan kafafen watsa labarai, Mr Muyiwa Adekeye ya fitar a ranar Juma'a ta ce gwamnan ya amince da nadin ne bayan samun shawarwari daga masu zaben sarakuna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Ya ce Injiya Lere ne ya yi nasara cikin mutane biyar masu neman sarautar da masu zaben sarki na masarautar Lere suka tantance.

Takaitacen tarihin Injiniya Suleiman Lere

Sanarwar ta ce: "Sarkin mai shekaru 61 ya kamala karatun digiri na farko a bangaren Injiniya a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1985, sannan ya sake digiri na biyu a bangaren kasuwanci wato MBA a ABU a shekarar 2000.
"Ya yi aiki a kamfanin man fetur na kasa NNPC inda ya yi ritaya a Fabrairun 2020 bayan cikarsa shekaru 60 a aiki.
"Marigayi sarkin Lere Birgediya Janar Abubakar Garba Muhammad ya nada shi Madakin Lere a shekarar 2015."

KU KARANTA: Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

Takaitacen tarihin Rev. Habila Sa'idu

Adekeye ya bayyana, "An haifi sabon sarkin, Rev. Habila Sa'idu a ranar 30 ga watan Oktoban 1955 a Nindem a karamar hukumar Jema'a ya kuma yi makarantar frimare ta Godogodo daga 1961 zuwa 1967.
"Daga nan ya tafi kwallejin ECWA Bible Kagoro daga 1976 zuwa 1980, sai ECWA Seminary Igbaja, jihar Kwara daga 1985 zuwa 1988, sai ECWA Seminary Jos daga 1998 zuwa 2001.
"Daga 2007 zuwa 2013, ya tafi Asbury Theological Seminary Wilmore a kasar Amurka."

Gwamna El-Rufai taya Sarkin Lere da hakimin Godogodo murna gadon sarautar kakakinsu ya kuma bukaci su yi amfani da matsayinsu wurin kawo zaman lafiya da cigaba.

A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel