Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

  • Wani mutum a unguwar Rigasa, Kaduna ya yi ƙarar ƙaninsa a kotu kan zarginsa da ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu
  • Wanda ya yi ƙarar, Sani Abubakar, ya yi ikirarin cewa mahaifinsu ya bar wasiyyar a gina masallaci a wani filinsa amma ƙaninsa da filin ya faɗa a matsayin gadonsa ya gina gida
  • A ɓangarensa, wanda aka yi ƙarar, Adda'u Ahmed ya ce bai da masaniya kan wannan wasiyyar da yayansa ke iƙirarin cewa ya saɓa

Wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Abubakar ya ce Shuaibu ne ya raba gadon sannan ya bada masallacin ga Ahmed.

"Ina son kotu ta umurci Ahmed ya kwace kayansa daga masallacin," in ji shi.

Yayin da suke kare kansu, wadanda aka yi ƙarar su sun ce ba su da masaniya kan ikirarin da wanda ya shigar da ƙarar ke yi, suna mai cewa a filin mahaifinsa Ahmed ya gina ɗakinsa.

KU KARANTA: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Abinda kotu ta ce game da karar da aka shigar

Bayan sauraran su, Alƙali, Malam Salisu Abubakar-Tureta ya umurci Abubakar ya gabatar da shaidunsa.

Abubakar-Tureta ya kuma ce kotun za ta ziyarci gidan domin gane wa idonta abin da ake rikicin a kansa.

Ya ɗage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 8 ga watan Yuli.

A wani labari daban, Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel