Cutar da daliba: Kotu ta ce malamin Jami’ar Jos ya biya diyyar N5m

Cutar da daliba: Kotu ta ce malamin Jami’ar Jos ya biya diyyar N5m

  • Kotun ta umarci jami’ar da ta biya dalibar diyyar N100,000
  • Jami’ar ta kori dalibar a ajin karshe na kammala karatun digiri na biyu
  • Daga cikin dalilan jami’ar na sallamar ta akwai rashin kwazo

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Jos babban birnin Jihar Filato, karkashin jagorancin Mai Shari’a M.H. Kurya ta umarci wani malami a sashen Tattalin Arziki na Jami’ar Jos, Mista Thaddeus Longduut, da ya biya N5million ga wata daliba da ke karatun digiri na biyu a fannin Tattalin Arziki, mai suna Georgia Davou, saboda cin zarafinta wanda ya sa ba ta kammala karatun ba.

Thisday ta rahoto cewa a shari’ar da kotun ta yanke hukunci a kai ranar 23 ga watan Yuni, ta umurci Jami’ar Jos da ta hanzarta ta biya mai karar N100, 000 a matsayin diyya, sannan ta sake maido da dalibar kuma ta sauya mata malamin da zai duba aikinta tare da tabbatar da cewa ta kammala kare aikin nazarin da ta yi a cikin lokacin da ya dace.

Lauyan mai karar, Gloria Ballason, a 2018 ta gabatar da bukata a kan wadanda ake karar kan korar dalibar daga karatun digiri na biyu kan zargin rashin tabuka abin kirki ba tare da bin tsarin makarantar ba, sannan ba tare da ba ta damar duba takardun sakamakon jarrabawarta ba, da ma rashin yi mata adalci lokacin da ta nemi makarantar da ta ba ta damar duba takardun sakamakon nata.

KU KARANTA: Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun

Cutar da daliba: Kotu ta ce malamin Jami’ar Jos ya biya diyyar N5m
Cutar da daliba: Kotu ta ce malamin Jami’ar Jos ya biya diyyar N5m
Asali: UGC

DUBA NAN: An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

Mai gabatar da karar ta kuma yi ikirarin cewa wanda ake kara na biyu, wanda ya kasance shi ne mai duba aikin dalibar, ya ci zarafinta sannan ya kawo mata cikas wajen kare wa na karshe na nazarin da ta yi.

Lauyoyin da ke tsayawa UniJos da Malamin jami’ar wanda lauya NV Denden ya jagoranta, sun yi ikirarin cewa kwazon mai gabatar da kara ya kasa cimma gwadaben makarantar da aka sanya, kuma kotun ba ta da ikon tsoma baki a harkokin cikin gidan da suka shafi jami'ar ba ta hanyar sauraron bukatar mai gabatar da karar ba na neman a ba ta damar duba takardun sakamakon jarrabawarta da makin da ta samu sannan a gabatar da tsarin bada makin dukkaninsu a gaban kotun ba.

Koda yake kotun ta ce duk lokacin da wata hukuma ta ki bin ka’idojin sauraren korafi bisa adalci, hakkin kotun ne ta cike gurbin, rahoton ya kara.

Wanda ake tuhuma ya bukaci a cire shi a cikin karar, amma aka ki amincewa da bukatar tasa, ya kasa gabatar da hanzarinsa kamar yadda kotun ta bukata, sannan ya kasa gabatar da wata shaida.

Kotun ta ce Malamin bai tabbatar da cewa dalibar ta fadi ba yayin da ta zana jarabawarta ta karshe kuma ta rubuta babi na karshe na nazarinta.

Ta kuma ce Malamin bai yi wa mai shigar da karar adalci ba a lokacin da ta gabatar da korafinta.

Sannan kotun ta umarci malamin jami’ar da ya gaggauta biyan dalibar N5m a matsayin diyya kafin ya yi yunkurin daukar duk wani matakin shari’a a kan hukuncin.

An sace Malaman jami'a

A bangare guda, Yan bindigan sa duka sace malamin jami'ar Jos (UNIJOS) sun nemi a basu miliyan N10m a matsayin kuɗin fansa kafin su sake shi.

Dr Lazarus Maigoro, shugaban ƙungiyar ASSU reshen UNIJOS, shine ya tabbatar da haka da hukumar dillancin labaran Najeriya (NAN).

Asali: Legit.ng

Online view pixel