An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

  • Duk maniyyacin da bai yi rijistan Hajji ba ya jira sai badi
  • An rufe damar rijistar yin Hajjin 1442 bayan Hijra
  • Sama da mutum dubu dari biyar suka yi rijista

Ma'aikatar aikin Hajji da Umrah a kasar Saudiyya ta rufe yin rijista ga maniyyata dake son gudanar da Ibadar Hajji na shekarar 2021.

Hakan ya bayyana ne a jawabin da hukumomin Masallatan Makkah da na Madina suka saki a shafinsu na Facebook Haramain Sharifain, ranar Laraba.

A cewar jawabin, mutum sama da 540,000 ne suka samu nasasrar rijista kuma cikinsu mutum 60,000 kacal za'a zaba.

Jawabin yace:

"An kulle rijistan aikin hajjin shekarar 1442. Sama da mutum 540,000 ne suka nema. Ranar Juma'a, 25 ga Yuni za'a sanar da mutum 60,000 da aka zaba."

KU KARANTA: Dalilin da Buhari da APC suka gaza a cikin shekara hudun farko — Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan

An rufe rijistan Hajjin Bana a Saudiyya
An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000 Hoto: Haramain Sharifain
Asali: Facebook

DUBA NAN: Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

Mazauna Saudiyya ne kadai za su Hajjin bana, Ma'aikatar Hajji da Umrah

Hukumomin kasar Saudiyya sun ce mazauna cikin kasar ne kadai za a bari su gudanar da aikin Hajjin wannan shekarar.

Ta ce mutum dubu 60 ne kadai za a bari su gudanar da ibadar Hajjin sakamakon annobar COVID-19 da duniya ke fuskanta a halin yanzu.

NAHCON ta tabbatar 'yan Najeriya ba za su je Hajjin bana ba, ta bayyana mafita

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa Masarautar Saudiyya ta soke aikin Hajjin mahajjata daga kasashen duniya na shekarar 2021.

Shugaban na NAHCON, Zikrullah Hassan, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Fatima Usara, jami'ar hulda da jama’a ta hukumar ta fitar ranar Asabar a Abuja.

Mista Hassan ya ce NAHCON na mutunta hukuncin da Saudiyya ta yanke game da wannan batun komai tsananin hukuncin ga hukumar da kuma maniyyata a duk duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng