Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun
- Tsare wani soja a caji ofis din tare da ’yan kungiyar asiri ya haddasa lamarin
- Sojojin sun shiga caji ofis din inda suka kwato abokin aikinsu da karfin tuwo
- Da farko ’yan sanda sun tsare wadansu da ake zargin ’yan asiri ne
An ji karar harbin bindigogi a yankin Oelawo a titin Ikirun da ke garin Osogbo, babban birnin Jihar Osun a ranar Talata lokacin da wadansu sojoji guda uku suka dirar wa wani caji ofis a yankin domin kwato wani abokin aikinsu da ‘’yan sanda suka tsare.
Jaridar The Nation ta ce karar harbe-harben ya jefa fargaba da zullumi a zukatan mazauna unguwar yayin da wadansu suka yi ta gudun ceton rai.
Wata majiya da ke kusa da ofishin ’yan sandan wacce ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa jaridar The Nation cewa ’yan sanda sun kama wadansu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne sannan suka tsare su a caji ofis din.
A cewar majiyar:
“Daya daga cikin wadanda ake zargin ’yan kungiyar asirin da aka kama dangin wani soja ne to da yammacin ranar Talata sojan ya je caji ofis din domin ya karbi belin dan uwan nasa.
‘’To a lokacin da yake tattauna batun belin da ’yan sandan, sai suka samu rashin jituwa inda ’yan sandan suka garkame sojan a cikin inda suka tsare ’yan kungiyar asirin.
"Koda yake, ya riga ya sanar da abokan aikinsa cewa an tsare shi a ofishin ’yan sandan."
KU KARANTA: Dalilin da Buhari da APC suka gaza a cikin shekara hudun farko — Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan
DUBA NAN: Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa
Bayanai sun ce wadansu sojoji guda uku, dauke da wukake sanye da riguna masu garkuwa na sojan sun dirar wa caji ofis din da misalin karfe 8 na dare domin su yi amfani da karfin tuwo su kwato abokin aikinsu da ke tsare.
Wata majiyar ta ce:
“ ’Yan sanda sun fara harbi cikin iska domin tsoratar da sojojin amma da suka lura cewa sojojin suna kan kudurinsu, sai suka yi harbi kan sojojin wadanda harsashin bai ratsa su ba.
“Sannan ne ’yan sandan suka ruga da gudu daga caji ofis din yayin da sojojin suka fatattake su daga wajen.
"Sojojin sun sake komawa caji ofis din inda suka sake abokin aikinsu."
Kakakin ’Yan sanda ya tabbatar
Kakakin ’Yan sandan Jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ya tabbatar wa jaridar The Nation faruwar lamarin.
Ta ce:
“Wadansu da suka yi ikirarin sojoji ne daga Ede sun tafi da wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne zuwa Barikin Soja na Ede. Mun yi kame-kame a kai. ”
Asali: Legit.ng